Thursday, 8 November 2018




Yan bindiga sun kai hari a jihar Yobe

Home Yan bindiga sun kai hari a jihar Yobe

Anonymous

Ku Tura A Social Media
'Yan bindiga sun kai hari a jihar Yobe

LABARAI DAGA 24BLOG
[post by samaila umar lamido ]
Rahotanni daga jihar Yobe a Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a garin Katarko da ke kusa da garin Damaturu.
Maharan sun abka garin ne da yammcin jiya laraba, inda suka bude wuta, lamarin da ya sa mutanen garin suka shiga daji.
Wani mutum da ya tsere cikin daji tare da iyalansa, ya shaidawa BBC cewa tun da misalin karfe 5 na yammacin jiya maharan suka fara harbin kan mai tsautsayi dlilin da ya sa suka gudu suka shiga daji.
Rikicin Boko Haram ya wuce - Buhari
Mun karya lagon Boko Haram - Buhari
An ga sauran ’yan matan Chibok da aka sace
Ya ce tare da jami'an tsaro suka gudu suka shiga daji a lokacin da maharan suke harbe-harbe.
"Mata da kananan yara sun firgita matuka inda suke cikin tashin hankalin rashin sanin abinda ke faruwa ga 'yan uwa da ke cikin garin," in ji shi.
Kawo yanzu ba a san ko akwai wadanda suka rasa rayukansu ko jikkata ba a harin.
Yobe na daga cikin jihohin yankin arewa maso gabashi da suka dade suna fama da hare haren Boko Haram.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: