Za a karbe kudin ajiya na bayar da belin Nnamdi Kanu
Mai shari'a Binta Murtala Nyako, ta bayar da umarnin a ajiye kudin a asusun kotun, ba asusun ajiya na gwamnatin tarayyar kasar ba, na TSA, kafin ranar da za a sake zaman shariar a ranar 28 ga watan Maris na shekara mai zuwa.
Mai shari'ar ta kuma yi barazanar cewa za ta bayar da sammacin kamo mata wasu daga cikin wadanda suka tsaya wa jagoran 'yan awaren saboda rashin bayyanar su a zaman kotun da aka yi
Shi dai Nnamdi Kanu, an yi masa gani na karshe ne a Najeriya tun a watan Satumba na 2017, kafin sojoji su yi wa gidan iyayensa da ke Umuahia babban birnin jihar Abia, dirar mikiya a lokacin farautar 'yan awaren na Biafra.
A watan da ya gabata ne wato Oktoba, ya bayyana a wani hoton bidiyo yana addu'a a Isra'ila, da kuma wata hira da aka nuna cewa gidan talabijin na Isra'ila ne ya yi da shi, ko da yake ofishin jakadanci na Isra'ilar a Najeriya bai tabbatar da cewa ya je kasarsu ba.
Waiwaye
Mista Kanu, wanda ke da izinin zama dan kasa na Najeriya da Birtaniya, ya kirkiri kungiyar People Of Biafra (Ipob), a shakarar 2014 domin neman kafa kasar Biafra.
"Idan akwai wani bangare na Najeriya da ke son shiga yankin na Biafra, to muna musu maraba, matukar sun yi amanna da karantarwar addinan Yahudu da Kiristanci, tsarin karantarwar da kasar Biafra ta ginu a kansa.
Shirin samar da kasar Biafra dai ba sabon abu ba ne.
A shekarar 1967, shugabannin kabilar Igbo sun ayyana kasar Biafra, bayan wani mummunan yakin basasa, wanda ya jawo mutuwar kusan mutum miliyan daya, amma an samu galaba a kan masu neman ballewar.
Mista Kanu, shi ne na baya-bayan nan a kabilar Igbo da ke fafutukar ci gaba da gwagwarmayar neman kafa kasar Biafra
0 Comments:
Post a Comment