Yaki sai da dabara: Buhari ya kaddamar da wani sabon wayon kamfen
Taura A yau, Alhamis, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar wani sabon salon yakin neman zabe mai taken "Buhari unity Band" domin shiryawa yakin neman zaben shekarar 2019 da za a fara cikin kwanaki 3 ma su zuwa. Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta tsayar da ranar 18 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da 'yan takarar shugaban kasa za su fara kamfen. Wata kungiya mai suna "Good Governance Ambassadors of Nigeria" ta bullo da tunanin salon yakin zaben. Sabon salon kamfen din mai taken BUB, a takaice, zai mayar da hankali ne wajen samar da wasu kawanyar hannu na roba da ke dauke da hotuna ko rubutun kamfen din Buhari. Yaki sai da dabara: Buhari ya kaddamar da wani sabon wayon kamfen
Sarki Sanusi Da yake kaddamar da irin wadannan kawanyar hannu a yau, Alhamis, a fadar shugaban kasa, Aso Rock, shugaba Buhari ya bayyana damuwarsa bisa yadda matsowar zaben shekarar 2019 ke haifar da fargaba a Najeriya. Kazalika, ya bayyana aniyar gwamnatinsa na tabbatar da hadin kai a tsakanin al'ummar Najeriya da kuma zamanta a matsayin kasa daya. "Da yardar Allah za mu cigaba da zama daya, al'umma daya," shugaba Buhari ya fadi a jawabinsa. Sannan ya cigaba da cewa, "kasar mu ta tsallake siradi mai yawan gaske, musamman wadanda ke barazana ga zaman mu a matsayin kasa daya mai al'umma daya, amma da taimakon Allah har yanzu muna nan a dunkule a matsayin kasa guda. "Tabbas har yanzu muna fama da kalubale ta fuskar hadin kan al'umma, amma za mu shawo kan dukkan mastalolin mu. "Kaddamar da wannan kawanya tamkar wani yunkuri ne na isar da sakon hadin kai a tsakanin 'yan Najeriya domin duk wanda ya saka shi ya zama jakadan hadin kan Najeriya," a kalaman Buhari. Jagoran kaddamar da salon kamfen din 'BUB', Mista Felix Idiga, ya ce sun bullo da wannan tunani ne domin wargaza shirin jam'iyyar adawa na yin yakin neman zabe bisa ta hanyar amfani da kabilanci da raba kan jama'a.
0 Comments:
Post a Comment