Thursday, 15 November 2018




Zan wallafa sunayen mutanen da suka bawa Oshiomhole cin hanci - Tsohon kakakin APC

Home Zan wallafa sunayen mutanen da suka bawa Oshiomhole cin hanci - Tsohon kakakin APC

Anonymous

Ku Tura A Social Media
[post by samaila umar lameedo]
Zan wallafa sunayen mutanen da suka bawa Oshiomhole cin hanci - Tsohon kakakin APC

LABARAI DAGA 24BLOG
- Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na APC, Timi Frank ya ce zai fitar da sunayen mutanen da suka bawa Oshiomhole cin hanci yayin zabukkan cikin gida
- Frank ya yi ikirarin cewa wasu 'yan takara ne da suka fadi zabukka suka bawa Oshiomhole cin hanci domin ya cire sunan wasu ya sauya da nasu
- Frank ya yi kira da shugaba Muhammadu Buhari ya dauki mataki a kan Oshiomhole tunda hukumar DSS ta sanar dashi batun karbar cin hancin
Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam'iyyar APC, Timi Frank ya yi barazanar cewa zai wallafa sunayen mutanen da suka bawa Adams Oshiomhole cin hanci da adadin kudaden da suka bayar yayin zaben cikin gida na jam'iyyar da akayi baya bayannan.
Ya kuma yi ikirarin cewa Oshiomhole ya karbi zunzurutun kudi sama da $50 miliyan daga hannun masu neman takara da 'yan takara.
Zan wallafa sunayen mutanen da suka bawa Oshiomhole cin hanci - Tsohon kakakin APC
A cewar Frank, galibin kudaden da aka bawa Oshiomhole sun bi ta hannun wasu mutane ne daga jihohin Imo, Zamfara, Adamawa, Ogun da sauran su.
DUBA WANNAN: Wani dan majalisa ya sake ficewa daga APC, ya bayar da dalilai
Wani rahoto na musamman da Sahara Reporters ta wallafa a ranar Alhamis ya bayyana cewa hukumar DSS ta rubuta wasika ga shugaba Muhammadu Buhari inda ta bukaci ya gurfanar da Oshiomhole bisa zarginsa da karbar a kalla $55 miliyan a yayin gudanar da zabukkan cikin gida.
Frank ya kallubalanci shugaba Buhari ya dakatar da Oshiomhole sannan ya bincike shi idan har yaki da rashawa da ya keyi na gaskiya ne.
A sanarwar da ya fitar a Abuja, Frank ya yi ikirarin cewa Oshiomhole ya karbi makuden kudin ne domin sauya sunnan wadansu yan takara da su kayi nasara da na wadanda suka fadi zaben cikin gidan.
Sai dai a bangarensa, Oshiomhole ya musanta karbar cin hanci kuma ya bayyana cewa ba hurumin hukumar yan sandan farin kaya (DSS) bane ta rike binciken rashawa, ya ce wannan aikin EFCC da ICPC 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: