Monday 10 December 2018




Bai kamata a sake zaben Buhari ba -Inji Dattawan Arewa

Home Bai kamata a sake zaben Buhari ba -Inji Dattawan Arewa

Anonymous

Ku Tura A Social Media
tw
Kungiyar dattawan arewacin Najeriya
da ake kira
Northern Elders Forum ta
sanar da janye goyon bayanta ga sake
zaben shugaba Muhammadu Buhari. Shugaban kungiyar Farfesa Ango
Abdullahi ya shaida wa
BBCHAUSA cewa sun
yanke wannan shawarar ne saboda abin
da ya kira "ba wani abin cigaba da
Buhari ya yi wa arewa a kusan shekaru
hudu na mulkinsa." "Buhari ya gaza wajen magance talauci
da matsalar ilimi a arewacn Najeriya," in
ji Farfesa Ango. Ya ce arewacin Najeriya ne dandalin
talauci, kuma yankin ne ya dage wajen
ganin Buhari ya lashe zaben shugaban
kasa a 2015.
Amma Injiniya Khailani Muhammad
shugaban 'yan a kasa a tsare na kasa na
shugaba Buhari, ya yi watsi da ikirarin na
Farfesa Ango. Ya ce su Farfesa Ango sun yi hakan ne
don kansu ba da yawun mutanen arewa
ba, "Sai don abin da Atiku zai dauka ya
ba su." Ya kuma ce Buhari yana iya kokarinsa,
domin ba lokaci daya ake yin gyara ba sai
an dauki lokaci. A cikin bayanin da Farfesa Ango ya yi ya
ce "ba mu yaba da ayyukan da shugaban
kasa da gwamnonin arewa suka yi ba na
gwamanatin APC." "Mun sa ran za a samu canji bayan Buhari
ya ci zabe amma mun zuba ido ba mu ga
komi ba." "Idan ba wani abu ya canza ba, bai
kamata a goyi bayan shi idan ya sake
neman zabe ba." Farfesan ya kara da cewa "idan ma
Buhari bai ci ba, wani dan arewa ne zai ci
zaben." Ya ce sun dade da yanke shawarar juya
wa Buhari baya tun watanni da dama da
suka gabata kafin yanzu. "Saboda haka ya kamata a ba su notis, za
mu fadakar da mutanen arewa cewa sun
gaza saboda haka idan lokaci ya dawo
suna neman kuri'a a ki zabensu." Amma a martaninsa, Injiniya Khailani ya
ce " Idan su da ke kiran kansu dattawa
sun damu da matsalolin arewa me ya sa
ba su tashi tsaye ba wajen an tayar da
masaku da masana'antun da suka
durkushe....@BBC
Tamabaya Mai Karatu Shin Yaya wannan Zancen Yake gaskiyane koko kawai dan Neman kudi sukayi hakan??

Yi kasa Dan ajiye ra'ayinka 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: