Wani yaro mai shekara takwas wanda ke yin bayani a kan kayan wasan yara a shafinsa na YouTube ya zama na daya a jerin masu samun kudi a danadalin da dala miliyan 22.
Mujallar Forbes ta Amurka ta kiyasta cewa yaron mai suna Ryan mai shafin Ryan ToysReview ya doke Jake Paul da dala 500,000 a karshen shekarar da suka auna wadda ta kare a watan Yuni.
A kan wallafa bidiyo a kusan kowace rana, inda wani sabon bidiyon da Ryan ya fito a ciki yana tallata wani katafaren kwai ya sami masu kallonsa da suka zarce mutum miliyan daya daga Lahadi zuwa Talata.
Shafin The Dude Perfect kuma shi ne na uku da dala miliyan 20, in ji mujallar ta Forbes.
Wadanda ke kan gaba a YouTube
Matsayi Suna Yawan Samunsu
1 Ryan ToysReview $22m
2 Jake Paul $21.5m
3 Dude Perfect $20m
4 Daniel Middleton $18.5m
5 Jeffree Star $18m
6 Markiplier $17.5m
7 Evan Fong $17m
8 Jacksepticeye $16m
9 PewDiePie $15.5m
10 Logan Paul $14.5m
Kudaden da Ryan ya samu a bana sun nunka na bara bayan an cire haraji da kamashon da yake biyan lauyoyinsa da sauran masu yi masa hidima.
Da tashar NBC ta Amurka ta tambaye shi dalilin da yasa yara ke son kallon bidiyonsa, sai ya ce: "Saboda na iya nishadantar da su, kuma ni bai ban dariya ne".
Tun da iyayensa aka bude shafin nasa a watan Maris na 2015, bidiyon da aka wallafa an kalle su kusan sau biliyan 26, kuma shafin na da mabiya miliyan 17,300,000.
Mujallar ta Forbes ta kuma ce yana samun miliyan 21 cikin miliyan 22 ne daga tallace-talacen da a kan sanya a
0 Comments:
Post a Comment