Wata Sabuwa Wai Shi ya Koyawa Yariman Saudiyya Turanci
Home ›
›
Wata Sabuwa Wai Shi ya Koyawa Yariman Saudiyya Turanci
Ma'aikacin BBC wanda ya koyar da Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman Turanci a lokacin yana karami ya bayyana irin rayuwar da yariman ya rika gudanarwa ta dan gidan sarautar Saudiyya duk da cewa a lokacin ba a san shi ba sosai. Lokacin ina koyarwa ne a makarantar Al-Anjal da ke birnin Jeddah a shekarar 1996, sai kawai aka kira ni. Gwamnan Riyadh Yarima Salman bin Abdul Aziz Al Saud ya koma birnin Jeddah da iyalansa na wani lokaci, kuma yana bukatar malamin da zai koya masu Turancin Ingilishi. Mutumin da zai zama sarkin Saudiyya daga baya ya tuntubi makarantar da nake koyarwa, kuma babu bata lokaci sai aka tura ni zuwa fadar yariman domin in fara koyar da 'ya'yansa da matarsa ta farko ta haifar masa: Yarima Turki da Yarima Nayef da Yarima Khalid da kuma Yarima Mohammed. A lokacin gidana na wata unguwa mai tasowa. Kullum da misalin karfe 7 na safe a kan aika wani direba ya kai ni makarantarmu ta Al-Anjal, inda bayan an kammala karatu da misalin karfe 1 na rana sai direban ya kai ni fada. Da zarar an wuce kofar fadar da dakaru ke gadinta, motar da ta dauko ni kan wuce ciki ta gaban wasu maka-makan gidajen kawa da ma'aikata sanye da fararen kayan aiki ke lura da su. Akwai kuma motocin kawa masu yawa da aka ajiye su a gaban gidajen. Wannan ne lokacin da na ga motar nan mai suna Cadillac mai launin ruwan goro a karon farko Arewabestie.blogspot.com
0 Comments:
Post a Comment