[post by samaila umar lameedo]
Dalilin da ya sa Atiku ya kauracewa taron zaman lafiya
LABARAI DAGA 24BLOG
Dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana dalilin da ya sa ya kauracewa taron tabbatar da zaman lafiya a zaben 2019.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce bai san da taron ba domin ba a gayyace shi ba, kamar yadda kakakinsa Paul Ibe ya fitar da sanarwa a Twitter.
"Babu wani goron gayyata da Atiku ya samu domin halartar taron kulla yarjejeniyar ta zaman lafiya," in ji shi.
Sai dai kuma wanda ya jagoranci kulla yarjejeniyar, tsohon shugaban kasa Abdussalam Abubakar ya shaida wa BBC cewa sai da suka zauna tare da dukkanin jam'iyyun siyasar Najeriya aka cimma matsaya.
An tambaye shi game da ikirarin bangaren Atiku kan rashin gayyatar shi, sai tsohon shugaban ya ce "Me zai sa ba za mu gayyace shi ba, kuma me zai sa ba za mu gayyaci kowa ba?"
Muna zance ne yadda za a gaya wa mutane a yi siyasa ba da gaba ba, to me zai sa na dauki mutum guda na ce ba zan gayyace shi ba," in ji Janar Abdussalam.
Wata sanarwa da jam'iyyar PDP ta raba wa manema labarai, Jam'iyyar ta bayyana takaicinta na raashin halartar taron, tana mai cewa an samu matsalar samun cikakken bayani ne tsakanin jam'iyyar da kwamitin da ya shirya kulla yarjejeniyar.
Amurka da EU na son a rungumi kaddara 'kan Buhari da Atiku'
Da gaske EFCC na farautar 'ya'yan Atiku?
Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da wasu 'yan takarar da dama sun halarci taron kuma sun sa hannu a 'yarjejeniyar.
An sa hannun ne a kan idon malaman addinai da sarakunan gargajiya da kuma jakadu na kasashen Turai.
Abin da yarjejeniyar ta kunsa
Yarjejeniyar da tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya ke jagoranta ta bukaci 'yan takara da jam'iyyunsu su tabbatar da zaman lafiya a lokacin zabe da kuma bayan zaben.
Yarjejeniyar kuma ta bukaci a kaucewa duk wasu kalamai na batanci ga addinin wani ko kabila.
Sannan ta shafi kaucewa duk wani abu da zai kai ga haifar da tashin hankali a lokacin zabe.
Irin wannan yarjejeniyar ce aka kulla kafin zaben 2015 inda ake ganin ta taka rawa sosai ga sauyin shugabanci daga jam'iyya mai mulki zuwa ta hamayya ba tare da an samu wani tashin hankali ba.
A lokacin zaben 2015, tun kafin a kammala kidaya kuri'un zaben shugaban kasa, shugaba mai ci Goodluck Jonathan ya kira abokin takararsa Muhammadu Buhari ya amsa shan kaye.
Yanzu kuma ana ganin kauracewa taron kulla yarjejeniyar da dan takarar adawa Alhaji Atiku Abubakar ya yi babban kalubale ne ga samun nasarar yarjejeniyar a zaben na badi.
Ko da yake tsohon shugaban ya ce baya jin rashin zuwan dan takarar na PDP ma hamayya zai shafi ingancin yarjejeniyar da aka kulla.
Wednesday, 12 December 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Rahotanni: INEC ta bayyana Muhammadu Buhari gagarumar nasara a shekarar 2019.Rahotanni: INEC ta bayyana Muhammadu Buhari gagar
Wasu 'yan APC hudu da aka kama tare da takardun jefa kuri'a, bindigogi a Legas NATIONAL NEWS. Wasu 'yan APC hudu da aka kama tare da takardun j
Gudun Shari'ar Kasa a Kullum Kamar yadda Kotun Koli ta Tarayyar Tarayya ta ba da umurni ga sabon zabe a jihar Kano. Gudun Shari'ar Kasa a Kullum Kamar yadda Kotun Ko
Abinda Atiku ya ce bayan da Hukumar INEC ta dage zaben 2019Abinda Atiku ya ce bayan da Hukumar INEC ta dage
Zaben: Kwamishinan 'yan sandan Kano ya kashe' yan siyasa - GandujeZaben: Kwamishinan 'yan sandan Kano ya kashe' yan
Buhari ya samu kashi 9 daga cikin 23 a cikin Sakkwato, Atiku 3.Buhari ya samu kashi 9 daga cikin 23 a cikin Sakk
0 Comments:
Post a Comment