[post by samaila umar lameedo]
Saduwa a mota ba ta keta dokar Najeriya ba - 'Yan sanda
LABARAI DAGA 24BLOG
'Yan sanda a Najeriya sun ce yin jima'i cikin mota a bainar jama'a ba laifi ba ne.
Babban jami'in ofishin sauraren korafin jama'a na rundunar 'yan sandan ne Abayomi Shogunle ya fadi haka a yayin da yake amsa tambayoyi a Twitter.
An tambayi jami'in ne "ko laifi ne yin jima'i a cikin motarsa?" Sai ya ce "ba laifi ba ne" amma idan an kiyaye wasu sharudda.
Jami'in ya ce "jima'i cikin mota ba laifi ba ne a Najeriya, idan wurin da ake yi ba wurin ibada ba ne, kuma wadanda ke yi sun haura shekara 18".
"Kuma da yardar dukkanin bangarorin da ke aikatawa, kuma Mace da Namiji ne."
Ya kuma ce idan mutum har na fuskantar barazana a yayin aikata jami'in a mota, yana iya sanar da 'yan sanda.
'Yan sandan Najeriya baki har kunne saboda karin albashi
Makiyayan Mali ne suka shigo Sokoto - 'Yan sanda
Wadannan bayanan na jami'in 'yan sandan ya ja hankali sosai a kafofin sada zumunta, inda ya samu tsokacin mutane sama da dubu 100.
Kalaman sun janyo yabo da suka, yayin da wasu ke cewa ba dukkanin 'yan sanda ba ne suke sane da haka, domin sun sha kame mace da namiji da suka kebe mota.
Masu suka kuma na cewa hakan ya saba wa al'adar tarbiya a Najeriya.
Za a dai ci gaba da muhawara kan wannan batu a kasar.
Wednesday, 12 December 2018
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Shugabannin 'yan sanda 4 mafi girma za a iya tilasta su kamar yadda IGP Adamu ya daukaShugabannin 'yan sanda 4 mafi girma za a iya tila
Gwamnatin ganduje ne ta fara kammala ayyukan da ta gada Gwamnatin mai girma Dakta AbdullahiUmar Ganduje O
MALAMAN ALKUR'ANI SUN YI JAN KUNNE GA TASHAR AREWA24 Cikin Shirin (DADIN KOWA)Muna kallon shirin dadin kowa Muna kallon yadda k
SOjoji sun Kashe wata yar NYSC APC a cikin Bonny, Rivers State SOjoji sun Kashe wata yar NYSC APC a
Kotu: Kotun ta baiwa Melaye belinKotu: Kotun ta baiwa Melaye belinSanata mai wakil
CJN, Mohammed ya yi rantsuwa a cikin shugabanni 250, mambobi ne na Kotun Tsarin MulkiCJN, Mohammed ya yi rantsuwa a cikin shugabanni 2
0 Comments:
Post a Comment