Mai Shari’a Valentine Ashi ta Babbar Kotun Tarayya da ke Apo, Abuja, ta bai wa jami’an EFCC, SSS da ‘yan sanda kwanaki uku daga jiya Talata, 4 Ga Disamba, cewa su kamo tsohuwar ministar harkokin man fetur a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan, Diezani Alison-Makueke.
Wannan umarni ya zo ne bayan da lauyan EFCC, Msuur Denga, ya roki kotun ta bayar da iznin a kamo Diezani, ta hanyar bayar da takardar iznin a kamo wanda ake zargi, wato ‘arrest warrant’.
Ya ce ta haka ne kawai za a iya gurfanar da ita a gaban kotu ta amsa tuhumomin da ake yi mata.
EFCC ta ce tun a ranar 3 Ga Oktoba, 2013 wata kungiyar kishin hana cin hanci main suna CACOL, ta kai rubutaccen korafi a kan Diezani cewa ta shiga cikin harkallar cuwa-cuwar makudan kudade a wasu ciniki da ta gudanar a madadin gwamnatin tarayya.
Ana zargin ta tare da tsohon shugaban kamfanin Atlantic Energy Drilling Company, Jide Omokore.
Sannan kuma ana tuhumar su da karbar kyautar wasu maka-makan gidaje birjik a Ikoyi, Lagos da Tsibirin Banana a Lagos.
Kotu ta nemi a kamo su a gurfanar da su a ranar 25 Ga Fabrairu, 2019.
Premiumtimeshausa.
0 Comments:
Post a Comment