Kungiyar Valencia Ta Bada Rance Dan Wasanta Jeison Ga Barcelona
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake
kasar Spain ta karbi rancen dan wasan baya, daga kulob din
Valencia mai suna Jeison Fabián Murillo zuwa karshen kakar
wasan bana 2018/2019.
Valencia ta bai wa Barcelona aron dan wasan bisa yarjejeniyar
kungiyar, ta Barcelona za ta saye shi idan ya taka rawar gani,
kan kudi Yuro miliyan 25.
Kungiyar ta Valencia ta karbo Murillo, ne daga Inter Milan a
matsayin aro, a
shekarar 2017 daga baya ta amince da sayen sa inda ta biya
kudin Yuro miliyan £13 a mazaunin dan wasanta na din-din-
din.
Sai dai dan wasan ya buga wasanni uku kacal a kungiyar ta
Valencia, shine wasan da ta buga da Juventus da Celta da
kuma Ebro, daga bisani 'yan wasa irin su Garay da Paulista da
kuma Diakhaby suka ajiyeshi a bince, sakamakon sun fishi
taka leda.
Dan wasa Fabián Murillo dan kasar Colombia, ya taka leda wa
kasarsa cikin gasar Copa America, a shekarar 2015/2016 inda
Colombia ta kare a matsayi na uku.
0 Comments:
Post a Comment