Saturday 1 December 2018




Lamarin yiwa yammata fyade a Sudan ta Kudu yayi kamari

Home Lamarin yiwa yammata fyade a Sudan ta Kudu yayi kamari

Anonymous

Ku Tura A Social Media

Kungiyar likitoci masu ba da agaji ta kasa da kasa (MSF) ta koka kan irin wani irin mummunan cin zarafin mata da yara ta hanyar fyade kwanaki 10 da suka gabata a arewacin Sudan ta Kudu.

A wata sanarwa MSF ta ce ta bayar da kulawar ggaggawa da kuma shawarwari ga mata da 'yan mata 125 da aka yi wa fyade ko aka yi musu fashi ku kuma aka yi musu duka a yankin Rubkona.

Hakan dai na nuna cewa lamarin ya yi kamari, idan aka kwatanta da mutane 104 da aka ci zarafinsu kuma suka nemi taimako daga MSF cikin watanni 10 na farkon wannan shekara.

Wasu da aka ci zarafinsu dai yara ne 'yan kasa da shekara 10, yayin da sauran kuma suka haura shekara 65.

    'Bugaggen likita' ya kashe mai jego da jaririnta yayin yi mata tiyata
    Mata 100: 'Mata 137 makusantansu ke kashe su kullum a duniya'
    Yadda matan Najeriya ke shan wahala a Jamhuriyar Nijar

An ce masu kai musu farmakin suna yi musu fashin abubuwan da suke dauke da su, da suka hada da kudi, da tufafi, da takalmi, sannnan kuma suke lalata katinsu da ake amfani da shi wajen karbar tallafin abinci.

Kungiyar MSF ta ce yawan mutanen da ake yi wa fyaden, ya yi daidai da yawan mutanen da suka rasa muhallansu, da suke neman tallafin abinci a yankin.

Sun ce a yanzu haka mata suna tafiya ne cikin gungu saboda tsaro, sai dai duk da haka ana yawan kai musu farmaki.

Yakin basasar da ake yi a kasar ta Sudan ta Kudu ya tilastawa kusan mutum miliyan hudu fita daga gidajensu, kamar yada shirin samar da Abinci da Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana, yayin da Majalisar ta Dinkin Duniya ta ce akwai wasu mutane 40 da watakila ke da hannu a laifukan yaki, da kuma cin zarafin jama'a.

@bbchausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: