A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta zargi hukumar agajin da horarwa da kuma tura 'yan leken asirin Boko Haram
Batun dakatar da ayyukan UNICEF din dai ya zo da mamaki ga ita kanta hukumar, kuma ta shaida wa BBC cewa ta na tantance bayanan da zargin ya kunsa.
Boko Haram na iko da kananan hukumomi 17 a Borno - Sani Zoro
Sanarwar dai ta fito ne daga bangaren Operation Lafiya Dole, wani shirin rundunar na dakile Boko Haram.
Ta zargi hukumar da horar da mutane don yi wa ayyukan rundunar zagon kasa a kokarinsu na yaki da Boko Haram.
Rundunar sojin dai ta yi ikirarin cewa an yi wa 'yan leken asirin horon ne ran 12 da 13 ga Disamba a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Miliyoyin mutane a Arewa maso gabashin Najeriya ne Boko Haram ta daidaita, kuma da yawansu sun dogara ne da agaji domin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
A rahotonta na baya bayan nan, UNICEF ta yi kiyasin cewa kananan yara miliyan 4.5 ne ke cikin tsaka mai wuya a Najeriya
0 Comments:
Post a Comment