_*Asalinsu da taikaitacen Labarinsu*_
Abdullah wanda akafi sani da Abdul Hausa/Fulani ne mahaipinsa bahaushe mahaifiyarsa kuma Fulani."
"Yan garin Bauchi ne, mahaipinsa Adam su biyu ne wajen iyayensu dashi da kaninsa Ibrahim, sun taso cikin kulawar iyayensu, Kama daga nursery, primary, har secondary school sunyi maikyau, jami'ar su kuma a waje sukayi fannin business duk suka karanta, koda suka gama karatu suka dawo gida nejiriya nan suka Kama business gadan gadan shi Adam nakula da dukinyansu a garin bauchi inda sukeda da shaguna a kasuwanni da babban company'n su na sarrafa (pata). shikuma Ibrahim wajen sa kano yadawo da zama dan kula da company'n su na garin kano wato company'n sarrafa maganin sauro da company'n atamfofi."
"Business d'insu natafi cikin yardar Allah watarana Adam yafita zuwa kasuwa dan duba shagunansu na kasuwa k'wasam a cikin wata shagonsu na saida mayuka da costemetics yaga wata kyakyawar yarinya tunda yashiga shagon yake kallonta har saida tagama sayayya taxo biyan kudin yace tabari yabiyamata da farko yarinyar taso kinyarda amma ganin yadda ya nace yasata amincewa,har tasoma tafiya ya tashi ya bita yace tabasa lambar wayanta kuma dan Allah tafad'a mai sunanta."
"Batayi gardamava ta sanar dashi sunanta hadiza tavasa lambar wayan ta tafi."
"Ranar da dare ya kirata bayan yamata bayanin waye shi dakuma abinda ke tafe dashi."
"Cemasa tayi zatayi tunani akai, bai musataba ya yarje Mata kan tayi tunani nan sukayi sallama."
"Itama hadiza Yar garin bauchi ce amma ita Fulani suna zaune da iyayenta kuma sunada rufin asiri daidai Gwargwado."
"Bayan kwana biyu da yin haka hadiza ta amince da soyayyar Adam, Soyayya suke yi sosai kuma So mai tsapta Adam ke Mata."
"Vasu Kai ga jimawa Ba kowa nasu ya San da maganar su har manya sun shiga an tsaida ran aure."
"Bangaren Ibrahim shima kasuwanci Yana tafiya daidai kuma shima yasami nasa budurwan acan kano sun tsaida magana shima ya turo manya tare za'ayi aurensu da Adam duk lokaci daya."
"Wata daya maganar aka daura aurensu dukka inda shi Adam nan garin bauchi zasu tare da matarsa shikuma Ibrahim can kano zasu."
Kowannensu ya tare da matarsa zaman auratayya suke cikin jin dadi da kwanciyar hankali duka Mata yensu nasamin kulawa wajen mazajensu."
"Shekarar su daya da aure Allah ya alabarkacesu da samin ciki, duka hadiza da Asiya matar Ibrahim Nada ciki, sosai suke samin kulawa daga wajen Mazajensu."
"Cikinsu Nada wata Tara Allah ya saukesu lpy, inda hadiza ta sukuto da namiji itakuma Asiya Mace, ranar sunsha murna, haka aka yita zuwar musu barka yan uwa da abokan arziki."
"Ranar suna yaro yaci sunan kakansa Abdullah ake kiransa da Abdul, itakuma yarinya taci sunar kakar ta mace Zainab ake kiranta da hafiza."
"Abdul da hafiza sun taso cikin kulawar iyayensu gata sosai suke samu barin Abdul da yake namiji makarantar yayan masu shi aka sasu."
"Sun gama nursery,primary har secondary, suka zana jamb acan Nile university dake abuja suka sami admission dan can suka cika."
"Sun soma karatu lpy Abdul na karanta accountancy itakuma hafiza bsc nursing take."
"Abdul ya kasance namiji kyakyawa ajin farko a jerin maza, bayida hasken fata dan chocolate color ne yanada faffafan kirji, sumar kansa a kwance take kamar na larabawa, gashin girarsa a cike take kamar Mace yanada idana masu kyau da daukar hankali vakinsa a tsuke kamar mace gashi jajir abdul ya hadu na karshe."
'Gashi Sam baida tsiwa ko surutu inka gansa yana surutu toh da abbansa ko ummansa sai ko asiya matar Ibrahim, Mata dayawa na sonsa amma shi ko takansu baya bi."
"Sun kammala karatu sunyi vautar inda har sun soma aiki hafiza har tayi aure ta auri wani course mate dinta suna zaune a Kaduna."
"Abdul na aiki a UBA bank dake bauchi Yana samu sosai amma har yanxu ko budurwa baiyida."
"Hutu yaje wajen baffansa Ibrahim kano kuma da aikin da zai tayasa dan suna son hada company's din ya dawo duka garin bauchi shiyasa yaje yatayasa wasu abubuwa. "
"A wata alhamis ne yacewa umma asiya zai je siyayya store ya fita toh acan ya had'u da Mama."
_*Mama*_ yace ga Isma'il da rufaida, ita kad'ai Allah ya basu."
"Isma'il mahaifin Mama asalin dan Garin _*Bagudu*_ ne san'a ce ta dawo dashi garin kano da zama."
"Isma'il da matarsa rufaida duk yan garin bagudu ne auren hadi aka musu, sabida su a al'adance da kuma yarensu wato _*Fakanci*_ basa auren bare shiyasa aka had'a su aure."
"Wani alhaji ne da Isma'il ke saida masa kaya ya dawo da isma'il garin kano da zama bayan yabasa jarin naira dubu Dari biyar."
"Isma'il ya kasance mutum mai rikon gsky da amana, suna saida wa alhajin kaya ne a manya manyan shagunan sa idan isma'il ya dage yazauna tsayin daka wajen rikewa alhaji amanar da ya bar musa na shagonsa."
"Ire iren kyawun halayyen isma'il da tarbiyyansa yasa alhaji jin son isma'il har ya kaiga basa nasa jarin bayan ya daukesa ya kaisa kano ya budemasa shagon sai da atamfa, Sanadiyar barinsa garin _*bagudu*_ kenan ya dawo nan kano."
"Dawo warsu kano da diyarsu wato Mama nan akasata makaranta, makaranta mai kyau akasata tundaga primary har secondary duk a private school tayi."
"Isma'il na samu Ba laifi dan shagonsa yayi albarka ya cika dam da kaya ga customers dayake samu alhamdulillah."
"Mama ta kasance kyakyyawa ajin farko dogowace, wankar tarwad'a tanada gashi mai tsayi, bakinta karami kuma a tsoke yake kalansa launin pink color, akoi manyan idanu ga uban eyelashes haka kuma tanada cikan eyebrow (gira) har suna Neman had'ewa, figure 8 ce ita mai kirar kalangu shape na coca kola, kirjinta a cike yake dam da dukiyar Fulani gasu a tsaye kamar an hura balu, mazauninta (hips) shima Masha Allah tanada shi dadai gwargwado, Mama kenan matashiya yarinya mai jini a jika Yar 18yrs ce."
"Ta gama secondary school inda take diploma a BUK ta Fannin biochemistry."
"Tun lokacinda Mama ta Kai Mace mahaipinta ke kwabarta da karta sake ta kula samari,."
"Dawannan kalamai da mahafinta ya Mata ya sa kwata2 Bata bi takan samari ko sun Mata magana sai dai tabasu hakuri ta nuna musu an Mata miji haka suke hakura da ita.'
"Da farko a B.u.k akoi wani Gaye dayayi approaching dinta ta nuna masa bata yi."
"Amma sabida naci irinta gayen har yasa tasoma kulasa."
"Tun basuyi nisa da soyayyaba, watarana gayen yaje gidansu zance nan mahaipinta ya gansu ya cima gayen mutunci kuma yaja masa kunne da ya fita hanyar yarsa dan da mijinta, jiki sanyayye ya bar kofan gidansu Mama."
"Koda baffanta yashiga gida duka yamata ranar na fitan hankali har saida yaga numfashinta ya soma daukewa kan ya barta."
"Taci kuka sosai har ta godewa Allah ranar "
"Washegari baffanta yahanata zuwa school, va yadda ummanta batayiba amma yaki Yar jemata haka saida tayi good one week a gida kan ya barta ta soma zuwa bayan ya ja Mata kunne da ginda yamata sharudansa."
"Yakuma sanar da ita baxai yarje da aurenta wa wani yareba face _*yaren fakanci*_ "
"Tundaga wannan lokacin mama ta daina kula samari har kawo Rana ita yau da Allah ya hadata da Abdul."
"Lokacind Abdul yafurta yana sonta taso taki amincewa saidai ina tuni zuciyarta ta aminta da soyayyar Abdul."
"So! So!! Cuta, So bala'i, so matsifa ,so guba, So dafi, Mama tayi nesa a son Abdul bata jin Kira, yanxu tana ganin zata iya tunkarar mahaipinta da maganar Abdul duk tasan akoi aiki babba amma yazatayi."
_wannan kenan_
.
Abdul ya koma garinsu na bauchi da yake daman gurin kanen mahaifinsa ne ya je, a can ne ya hadu da Mama wato garin kano, bayan Abdul ya dawo gidansu bai bari yayi kwana koda daya bane ya je ya sanar da mahaifinsa zancen Mama, ya kuma gaya masa dukkanin abinda ya shafi rayuwarta. Mahaifin Abdul yana matukar son abdul hakan yasa yake masa komai yake so, bayan yaji zancen Abdul ya kuma amince da abindaAbdul ya zo masa dashi.
Mahaifin Abdul ya tura kannensa wurin neman auren d’ansa Abdul da Mama. Bayan iyayen Abdul sun je gidansu Mama neman auren Mama, mahaifinta yayi musu walakanci sosai wanda kare ma bazai daukaba, yakuma sanar dasu kancewa baxai bada auren ‘yarsa ga wani yareba face yaren FAKANCI.”
“ bayan sun dawo sun sanar da mahaifin Abdul abinda duk ya faru shima kuma ya nuna bakin cikinsa sosai da faruwar wannan al’amari tare da sanar da Abdul halin da ake ciki, hade da Jan kunnnsa kan yaxama dole yafita hanyan Mama inyanason farincikinsa, toh kawai Abdul yace amma bayajin zai iya.”
Abdul yaje dakinsa ya kwanta yana jimamin wannan al’amari, yana kwance ya dauko wayarsa ya kira masoyiyarsa Mama, kamar jira take yana bugawa sau daya wayar tayi ringing Mama ta dauka, tana dauka abdul yaji ta tana shesshekar kuka, cikin yanayin damuwa shima yace da ita “Tawa me yasa kike kuka?” muryarta a sarkake tace “me zaisa bazan yi kuka ba, daman zuwan wannan rana nake gudu a rayuwata, da ganin wannan rana dama mutuwa tazo ta daukeni kafin zuwanta…” “kidaina fadan haka, ai ni bana tunanin rabuwa dake saboda nasan rabuwa dake abune wanda bazai yuyu ba, tunanina kawai ya za’ayi mu kasance a tare, ni da ke tamkar haduwar gulbi da teku ne wadanda ba zasu taba rabuwa ba” Abdul ne ya katsewa Mama Magana tare da fadan haka, sai kuma ita tace “raba rayuwata da kai tamkar raba kifi ne da ruwa wanda babu tabbacin rayuwarsa idan ya fito ruwa, haka nima idan akace a raba zuciyata da soyayyarka to tabbas zan iya mutuwa” sai yayi murmushin karfin hali yace “ai rabuwa takan zo ne ga masoya a bisa kaddara, mu kuma tamu soyayya babu kaddarar rabuwa acikinta, kaddara daya itace mutuwa, amma raba zukatan mu da soyayyar junan mu abune wanda bazai yuyu ba, wallahi Mama ko ni akace na ciro soyayyarki acikin zuciyata bazan iya ba, ballai wani daban ya cireta, gangar jikin mu ne suke son rabawa amma bazasu iya raba soyayyarmu ba, ki daina zubar da hawayenki domin kuwa ni naki ne” sai tace
“wannan dalilin yasa zuciyata take alfahari dakai, domin kaine ka zamo sa gudun duk wani bakin ciki da ya tunkaro zuciyata tareda maye farin ciki a gurbin bakin ciki, tabbas kafin nayi waya dakai zuciyata tafarfasa take tamkar ana gobara acikinta, amma yanzu sakamakon jin kalaminka da tabbacin zaka kasance dani komai tsanani. Lokaci daya naji zuciyata ta dawo tamkar ba wani abu da yake damunta tare da bayarda jin dadi ga sassan jikina yanzu banjin komai yana damuna” “kawo wayar nan ‘yar iska” Mahaifinta ne yayi mata wannan Magana cikin tsawa lokacin da ya tarar da ita tana waya da Abdul, ya karbe wayarta tare da cigaba da yimata fada daga karshe yayi mata sharadin kada ta sake fita waje.
“Jikin Abdul ne yayi sanyi lokacin da yaji sautin mahaifinta yayi wannan Magana tare da karbe waya ya kashe. Lokaci daya Abdul yaji ya kasa tsayuwa da kafafunsa ya shiga tunani iri-iri, sai kuma ya tashi ya yunkura zuwa waje don tunkarar garinsu Mama, yana kai bakin kofar dakinsa ya tarar da mahaifinsa a tsaye, sai mahaifinsa ya dubesa cikin harara yace “bani makullin motar nan” ya mika hannunsa zuwa ga Abdul, cikin sanyin jiki Abdul ya dauko makullin motar daga cikin aljihunsa ya bashi, sai kuma Babansa ya sake cewa.”
“yanzu sai kaje duk gidan uwar da zaka je, kuma ina mai shaida maka cewa daga yau babu kai babu zuwa ko ina, idan kuma ka fita, idan ranka dubu ne sai dukansu sun bace” sai yayi tsaki ya juya ya tafi.”
“ Abdul ya koma cikin daki yana zubar da hawaye tare da sake kiran Mama amma yaji wayarta a kashe, lokaci daya ya shiga damuwa, a haka ya kasance cikin damuwa da bakin ciki.”
“Tsakanin Abdul da Mama kowa ya kasance cikin bakin ciki da damuwa tare da tunanin halin da dayansu yake ciki, amma babu mai jin labarin wani saboda kowa yana gidan an tsare”.
“cikin haka kawun Abdul na kano ya dawo bauchi da zama duka.”
“haka rayuwarsu taci gaba da gudana cikin yanayin bakin ciki da rashin jin dadi, duk Abdul yashiga wani yanayi, ga gidansu an daukemasa wuta, aunty asiyace kadai ke kwantar masa hankali da sasa cin abinci dan tana matukar tausayawa sirkinta Abdul."
"Haka Mama duk gidan jiyane itama....
“Mama ce ta shigo cikin gidansu Abdul tana zubar da hawaye, tana shigowa ta tarar da Mahaifin Abdul zai fita, sai ta durkusa agabansa tana kuka, ta dubesa tace.
“Abba dan Allah ku taimaki rayuwarmu wallahi bazan iya rayuwa babu abdul ba, idan kuka rabamu hakan zai sanadiyar halakarmu, ka tausaya muna”.
“cikin yanayin fushi Mahaifin Abdul ya dubi Mama yace “Wai ke bazaki ji maganar iyayenki bane, tunda har suka nemi su walakanta mu, ba zamu yarda da wani zancen auren ku ba, mu Hausawa bamu ce D’an mu bazai auri Fakanci ba, amma su zasu ce ba zasu aurar da ‘yarsu ga hausawa ba, dan haka ki tashi kibar gidan nan”
“ sai Mama tace “Abba kayi hakuri da duk abinda suka gayamuku, wallahi acikin rashin sani ne, basu san irin wahalar da zuciya take ba, aduk lokacin da ta rasa abinda take so, ni zan zauna tare daku, bazan iya komawa gida ba.”
“Kibar gidan nan nace tun kafin raina ya sake baci” Mahaifin Abdul ne ya fadi haka cikin fushi.
“Abdul na daki kwance ya jiyo muryar masoyiyarsa Mama, da hanzari ya fito ya tarar da Mahaifinsa yana korarta, sai yayi sauri yaci gaban Mama, sannan yazo inda Mahaifinsa yake ya durkusa tareda Mama, ya kalli mahaifinsa yace “Abba ka dubi irin halin da wannan yarinya take ciki, ka dubi irin halin da na shiga a lokacin da kazo ka gayamin iyayenta sun ce ba zasu bani aurenta ba, ka dubi irin azabar da zukatan mu suke ciki na rashin amincewarku. Dan Allah ku daina zancen Yare atsakanin soyayyarmu, wallahi ina sonta kuma bana tunanin zan iya sake son wata bayan ita, dan Allah Abba kabarta ta zauna anan har lokacin da iyayenta suka gane kuskurensu suka amince da auren mu” sai Mahaifinsa yace “idan kai bakada hankali to ni inada, sannan yanzu koda iyayenta sun amince da aurenku to ni bazan amince ba, kuma babu kai babu ita, idan kuma kace sai ita zaka aura to sai dai ka sake wani uban amma bani ba” sai kuma ya dubi Mama yace “ke kuma kibar gidan nan nace tun kafin ki fuskanci walakancin da baki yi zato ba” sai Mama ta tashi tsaye da nufin fita daga cikin gidan, amma kafin ta fita sai ta dubi Abdul tana Kuka tace “Abdul Duka ko Zagi basa fitar da sonka daga cikin zuciyata koda a bangarenka ne ballai bangaren iyayenka, dan haka zan tafi amma kasani tafiyata bata nufin rabuwarmu dakai ba, dan kuwa nasan rabuwarmu dakai abu ne wanda bazai taba yuyuwa ba har abada, sannan wannan korar da iyayenka suka yimin bazan ga laifinsu ba, kuma bazan tafi da haushin su ba, na dauki wannan abin kawai yana daga cikin kaddarar rayuwata” sai kawai ta juya ta tafi........
"Bayan ta fita Abdul ya dubi Mahaifinsa, sannan ya dubi Ummarsa dake gefe tana kallonsa cikin yanayin tausayi, bai cewa kowa uffan ba ya shige daki. Mahaifin Abdul ya dubi Mahaifiyar Abdul yace “Hajiya kada ki yarda yaron nan ya fita daga cikin gidan nan, dan nasan idan ya fita zai iya bin bayanta su tafi tare” sai Hajiya kada kai tace “to Alhaji insha Allahu zan kiyaye” sai Alhaji ya fita cikin gidan fusace.
***BAYAN SATI DAYA***
Alhaji ya fito firgice daga cikin dakin Abdul inda ya tarar da Hajiya tana shirin shiga dakinta, cikin kakkaurar Murya yace da ita “Hajiya shin ina Abdul ya shiga kwana biyu bana jin motsinsa, yanzu kuma na shiga dakinsa ban gansa ba?” sai Hajiya tace “wallahi Alhaji bansani ba, dan ni nayi zaton yana nan, kasan tun lokacin da abin nan ya faru Abdul ya daina fitowa waje ko abinci daina ci yayi, amma yana yuyuwa ya tafi wurin abokansa ne” sai Alhaji yace “Amma idan yaron nan guduwa ne yayi tabbas saina bata masa rai, ni zai rainawa da wayo, nace kada ya fita amma ya fita” Batare da Alhaji ya sake cewa wani abu ba, sai ya shige cikin dakinsa, itama Hajiya takarasa shigewa dakinta.
“Abdu ne acikin wani karamin Daki wanda da kagansa kasan dakin gaye ne, ko gayen wanda bayada ko sisi. Abdul na cikin dakin abokinsa mai suna Usman a kwance, sai ga Usman ya shigo cikin dakin yana tsaki, batare da yayi sallama ba ya je ya samu wuri ya zauna yaci gaba da tsaki, cikin yanayin mamaki Abdul ya taso zaune ya dubi abokinsa Usman yace “Wai abokina me yake damunka ne kake ta wannan tsakin haka?” sai Usman ya juyo da hankalinsa wurin Abdul yace “Wallahi Madam din nan ce ‘yar rainin wayo naje wurinta karbar bashin Garin Kwaki Naira Ashirin amma taki bani, kuma abin haushi agaban jama’a take fadan wai ina cin bashinta kullum amma bana biya”
Sai Usman ya nunfasa sannan yaci gaba da cewa “Allah Abokina in badan jama’a na kusa ba, dana mammake ta, abinda ya hanani aikata haka kuma ina tsoron nayi mata rauni narasa wanda zai bani bashi gobe” sai Abdul yayi dariya yace “To kai in banda abinka me zai sa kayi fushi da wanda ke taimakama yana baka bashi, ai dole kayi hakuri kabita a hankali” sai Usman yace “Yauwa abokina akwai Hamsin awurinka?” Abdul yace “Wallahi yau kwana biyar kenan ba kudi a aljihuna” sai Usman yayi tsaki yace “Ai kaji tsiyar, inama gudun haka amma baka gani, yanzu gashi awurinka an rasa Hamsin kaida kullum ‘Yan Dubu-dubu bugun Abuja ake gani a aljihunka, amma yau gashi ko Hamsin bakada. Na gayama ka koma gida ka hakura da wannan yarinya, sai kace ita kadai ce Macce a duniya, duk matan nan da suke duniyar nan karasa wacce zaka so sai ‘yar wani gari kuma wacce ma ba bahausa ba” sai Baffa yayi murmushi yace “daman ina jiran zuwanka dan muyi wata magana” sai Usman ya gyara zama yace “Yauwa Aboki ai daman nasan idan Talauci ya isheka zaka koma gida kadaina zancen yarinyar nan, dan yanzu wa yake ta soyayya ana ta Kudi” sai Abdul ya sake wani guntun murmushi a karo na biyu, sannan yace “Abokina ba wannan bane, kadai ga irin halin da nake ciki, kullum kunci baya fita daga zuciyata, so nake ka taimake ni ka rakani garin masoyiyata Mama, ko zan samu sukuni a zuciyata” “Wa! Ni zan raka ka, tab gaskiya banyi mafarkin na mutu ba, mu je gari bamuda kowa acan, sannan bamu da kudi, ka dubi yadda suka yiwa iyayenku da suka je ballai mu kananan alhaki, wallahi abokina nikam ina tsoron zuwa” Usman ne ya fadi haka yana zare idanu, sai Abdul yace “to miye kake tsoro da mutuwa, wallahi koda zasu kasheni ne sai naje, bazan hakurin rashin ganin Mama ba tsawon kwanaki, wai me yasa mutane basa fahimtar wanda ya fada tarkon soyayya, me yasa mutane suke tunanin cire so acikin zuciya haka yake da sauki kamar yadda ake cire sutura daga jiki, me yasa mutane suke tunanin masoyi zai iya hango wani wanda yafi masoyinsa bayan zuciya ta riga ta makantar da idanuwa daga hango kyawon wani wanda ba masoyinta ba, sannan ta toshe dukanin kofofin jin dadin sautin wani wanda ba masoyinta ba, Usman wallahi duk wanda yake cewa nabar Mama naso wata ji nake tamkar yana sambatu a barcinsa wanda bai san yana yi ba”.
Sai ya tashi tsaye sannan yaci gaba da cewa “Ban damu da zuwa da kudi don yin guzuri ba indai har zan samu kudin mota, dan na tabbata idan naje can nasamu ganin Mama to na wadatu da komai, ni fa koda yaushe idan natuna Mama sai naji damuwa ta yayemin, amma kuma idan natuna bata kusa dani sai naji tamkar ana dibar naman zuciyata, zan tafi idan kai bazaka rakani ba, kuma da yardar Allah zanyi nasara” sai Usman yayi ajiyar zuciya yace “Abokina shin ya akayi kayi nisa acikin soyayyar wannan yarinya kuma me yasa bazaka iya cireta a zuciyarka ba dan kasamu salama a rayuwarka tunda iyayenta sun ce bazasu baka aurenta ba” sai Abdul yayi murmushi yace “Wai abokina kai kuwa me yasa bazaka daina wannan sambatun ba, wa ya gayama Son Mama shiga zuciyata yayi, ai soyayyar Mama itace Zuciyar tawa gaba daya, sannan yanzu babu wata kofa a zuciyata ta karbar wata magana ko shawara ballai nace na tsaya nayi nazarin shawarar da kabani, sannan kwakwalta bata daukar zancen kowa a yanzu don ganin take ba dai dai bane, zancen Mama kawai take dauka dan shi ne dai-dai, kunnuwana kuwa basa tantance kowane irin yare mutum yake fada ballai su fahimci abinda ya fada, in ba maganar Mama ba, idanuwana kuma basa gane kalar kowa a yanzu ballai nagane muhimmancin mutum awurina in ba Mama ba, dan haka kayi hakuri da wannan sambatun naka saina dawo” sai Abdul ya fita, bayan ya fita Usman ya rinka kada kai yana magana shi kadai yana cewa “Lallai wannan yarinya ta mallake Abokina wannan So haka tab Allah ya kyauta” sai kuma Usman ya dawo tunanin yadda za’ayi ya samu kudin sayen garin Kwaki.”
“Hajiya ce ta isko Mahaifin Abdul zaune a dakinsa, itama tasamu wuri ta zauna, sai ta dubi Alhaji tace “Alhaji tsawon kwana biyar fa Abdul baya gidan nan, me zai hana aje anemo inda yake koda hankalin mu zai kwanta?” cikin fushi Alhaji ya dubeta yace “kwanciyar hankali kuma, ai sai in kece hankalinki yake atashe, ni kam hankalina akwance yake kuma ba inda zan je nemansa tunda ba karamin yaro bane, yaje duk gidan uwarda zashi, ai dai bayada wasu uwayen bayan mu, dan haka ki kwantar da hankalin ki duk inda yaje shi ne mai dawowa” sai Hajiya tace “Amma….” “Amma me?, ki canza zance idan zaki canza na gayamiki kidaina zancen aje anemo shi, shi da kansa zai dawo ya iske mu” Alhaji ne ya katsewa Hajiya magana ya fada mata haka. Sai Hajiya tayi tagumi batare da ta sake cewa komai ba.
0 Comments:
Post a Comment