Baffa yaje wurin Abokinsa Bashir ya ranto kudin mota wadan da zasu kaishi garin masoyiyarsa Mama wato Garin kano, Abdul ya shiga motar zuwa Kano tun daga Bauchi ba tareda yanada kudin cin abinci ba ya kama hanya. Suna tafiya acikin mota Abdul baya cewa kowa komai har suka isa garin Kano misalin karfe Goma Sha Daya na dare.”
“Bayan an Sauke Abdul tashar mota sai yayi tsaye yana tunani, ya rasa inda zai dosa, gashi dare yayi kuma gashi bai san kowa ba agarin sai gidan kawunsa gashi sun koma bauchi saikuma gidansu Mama, shi kuma gidansu Mama koda yaje ba zai samu shiga ba dan yana tsammanin sun kulle kofarsu. Yana cikin wannan tunani ne ya yanke shawarar yaje masallaci wanda ya hango a kusa dashi dan ya kwana in yaso idan gari ya waye yaje gidansu Mama dan ya ganta, haka kuwa yayi yaje masallacin ya iske shi a rufe, sai yayi kokarin budewa, yana budewa ya tarar an kashe wutar masallacin ya sussuda dan samun inda zai kwanta, yana zaunawa kafin ya kwanta ji kawai yayi ance “Ihu ga Barawon na kama” sai kawai aka kunna wutar masallacin, Abdul yaga mutane da yawa kowannensu da sandarsa, batare da bata lokaci ba suka farmasa da duka, Sahahu yana ihu yana fadan “Wallahi ni ba barawo bane” amma basu daina dukansa ba.
Bayan sun ga Abdul ya jigata, sai wani daga cikinsu ya dubesu ya daga hannu alamun su dakata, sai yace “Mu barshi a haka kunsan Liman yace kada mu dauki hukunci da kan mu, idan kuma muka kashe shi to lallai za’a yi muna hukunci mu ma, dan haka mu daure shi har gari ya waye mu nunawa Jama’a shi” sai su duka suka ce “hakane, kuma wallahi sai ya biya duk abinda ya dauka” sai kuma suka ajiye sandunan su suka dubi abdul suka ce “Barawon banza, kullum aka ajiye kaya saika dauka, to yau dubunka ta cika daman ance rana dubu ta barawo rana daya ta mai kaya” sai suka je suka samu wani ginshikin masallaci suka daure Abdul.
“Abdul yana daure jikinsa na zubar da jini, ba abinda yake tunani face wannan yanayi daya shiga, wani bangare kuma yana tunanin halin da zai tsinci kansa gobe, amma sai yayi addu’a ga Allah dan neman sauki.
Washe gari da Asuba an kammala sallar Asuba sai wani saurayi yazo kusa ga kunnen Liman yace “Allah gafarta Malam jiya da daddare an kama Barawon nan” sai Liman ya idar da addu’arsa, sannan ya dubi saurayin yace “Jeka ina zuwa”.
Liman ya fito waje don ganin Barawon, sai ya tarar da Yara da Manya sun zagaye Abdul, yana isa gurin suka bude masa hanya ya isa kusa ga Abdul. Yana zuwa ya dubi abdul sama da kasa yaga jikinsa jina-jina da jini, sai ya dubi nakusa dashi yace “me yasa kuka yi masa wannan dukan, to idan da ace ya mutu fa?” sai saurayin dake kusa ga Liman din yace “Allah gafarta Malam, wallahi saida nace adakata da sai dai aji mummunan labari” sai Liman ya dawo da kallonsa wurin Abdul yace “Kai kuwa me yasa kake wannan mummunan dabi’a, karasa abin sata sai kayan Dakin Allah, ka kuwa san mummunan zunubin dake tattare da aikata hakan?” Abdul na shessheka ya dubi Liman yace “Wallahi ni ba Barawo bane bako ne ni, jiya jiya na sauka a garin nan, na shiga masallaci ne dan nasamu wurin kwana ba dan sata ba, sai gashi wannan kaddara tafaru dani” sai Liman yace “Ta yaya zamu tabbatar da kai ba Barawo bane?” sai Abdul yace “Ni bansan yanda zani tabbatar muku da hakan ba, amma kuyi imani da Allah da cewa ni ba Barawo bane, idan kuma kuna shakka akan zancena, to kubarwa Allah idan har ni ne mai yi muku sata kada Allah ya bani abinda nakeso sannan ya debe muku alhakinku tun anan duniya kafin lahira, wallahi Malam ni ba Barawo bane” sai Liman ya dubesa yaga idanuwansa sun yi kwalla, sai Liman ya dubi saurayin dake kusa dashi karo na biyu yace “A yadda naga siffar yaron nan bangansa da alamar Barayi ba, kuma da nayi la’akari da maganganunsa na tabbatar da hakan, ku sake sa idan ma shi ne Lahira zai biya hakkin mu” sai Saurayin ya kwance Abdul.
Bayan an kwance Abdul sai ya dubi Liman yace “Nagode sosai kuma ina rokon Allah ya bayyana muku mai yi muku sata, sannan idan ya bayyana muku shi dan Allah kada kuyi masa yadda kuka yimin, domin kuwa kowane bawa da yadda Allah yake tsara rayuwarsa kuyi masa addu’ar shiriya awurin Ubangiji koda Allah zaisa sanadiyar addu’arku ya shiryu” sai Liman ya dubi wannan magana ta Abdul nan ya sake tabbatar da abdul ba Barawo bane. Sai Abdul yayi bankwana dasu, amma kafin ya tafi sai Limamin yace “Dan Samari naji kace kai bako ne kuma gashi jikinka ya jigata kuma tufafinka sun lalace sannan nasan kana bukatar abinci, dan haka muje gidana kayi wanka ka canza tufafi sannan kaci abinci” sai Baffa yayi guntun murmushi yace “Nagode Allah yasaka da alkhairi” sai Liman ya shiga gaba Abdul ya bi bayansa domin zuwa gidansa.
Da Abdul ya kammala komai na wanka da canza tufafi da cin abinci, sai yakara yin godiya ga Liman tareda yi masa bankwana ya tafi.
Tun da Abdul yabar gidan Liman bai tsaya ko ina ba sai kofar gidansu Mama, yana zuwa ya tsaya yana murmushi shi kadai yana jin farin ciki a zuciyarsa tun bai ga masoyiyarsa Mama ba, yana tsaye yana jiran yaron da zai aika, sai ga wata yarinya ta gifto Abdul ya tsayar da ita ya aika ta cikin gida don takira”
“ amma gabansa faduwa kawai yake don tunanin abinda zai faru dashi idan mahaifinta ya gansa, amma kuma sai ya kawar da duk wani tsoro da fargaba acikin zuciyarsa. Soyayya mai sauya tunani da nazari, Soyayya mai hana mutum ganin duk wata wahala ko walakanci akan masoyinsa, kamar yadda Abdul ya manta da dukan da yasha awurin mutanen gari sakamakon tuhumarsa da suke akan shi Barawo ne, duk wannan abin ya manta dashi abinda kawai yake tunani yaga fitowar masoyiyarsa.
Yana tsaye yana gyare-gyare, sai ga yarinya ta fito tace masa “an ce tana zuwa” sai Abdul yayi murmushi ya laluba aljihunsa da niyar yabata kudi amma sai bai ji ko sisi ba, sai dai yayi godiya gareta. Bayan yarinyar ta tafi sai ga Mahaifin Mama ya fito dan ganin mai kiran Mama.
Yana fitowa yayi ido biyu da Abdul, da hanzari Abdul ya durkusa kasa cikin ladabi ya gaida shi, amma yaki amsawa, sai ya dinga yiwa Abdul kallon takaici sannan daga bisani yace dashi “daman kai ne ka dawo, lallai yaron nan ko kai maye ne sai ka bar Mama, halan kunnuwanka basa jin abinda ake gayama ne, kai bakada zuciya ne?” Abdul na kasa batare da ya dago kansa ya dubi mahaifin Mama ba, sai yace “Baba kayi hakuri wallahi bana jin duk wata magana wacce ta danganci na rabu da Mama kuma bana gajiya da duk wani walakanci da zan fuskanta akan Mama haka kuma bana gajiya wurin rokonka dan Allah kabani Mama wallahi ina sonta” cikin fushi mahaifin Mama yace “to lallai kana tare da wahala, dan kuwa yau zaka fuskanci walakancin da ban taba yimaka ba, kabar kofar gidan nan tun kafin nasaka yara su koreka da jifa” sai Abdul yace “Baba wannan bazaisa naki sake dawowa ba, dan muddin ina lumfashi to bazan daina kasancewa duk inda Mama take ba koda za’a dinga yanka nama na” sai Mahaifin Mama ya kada kai yace “to shikenan zaka gani yanzu”. Sai kawai yabar Baffa ya shiga cikin gari domin kira yara.
Bayan wasu lokuta da tafiyar Mahaifin Mama cikin gari, Abdul na tsaye bakin kofar gidansu Mama bai je ko ina ba, sai ga mahaifin Mama yazo tareda gungun yara suna biye dashi, yana zuwa ya dubi yaran yace “kun gansa nan shi ne nakeson ku korar min shi da ruwan duwatsu” “Tau Baba” yara ne suka amsa da hakan, sai kawai suka dinga tsintar duwatsu suna jifar Abdul”
Abdul na tafiya yara na binsa da duwatsu suna kiran “Mahaukaci, ga Mahaukaci” haka suke fada suna jifarsa, bayan sun yi nisa da gidan su Mama. Abdul yana kare fuskarsa suna jifan jikinsa sai ga wani Mutum ya gifto yaga yara suna yiwa Abdul wannan aiki, sai yayi sauri yaje wurin tare da tsayar dasu, bayan sun dakata da jifar Abdul sai yace dasu “ku wadan mi irin ‘ya’ya ne haka, cewa akayi kuyiwa mahaukaci haka, dubi yadda kuka jimasa ciwo, ko tunda yana mahaukaci kashe shi zaku yi” sai suka yi dariya suka gudu batare da sun ce komai ba.
Bayan sun tafiyarsu, sai mutumin ya juyo dan ganin halin da Abdul yake ciki, sai ya tarar da Abdul ya suma, da sauri ya dauki Abdul ya tafi dashi gidansa, yana zuwa ya samu ruwa ya yayyafawa Abdul, bayan Abdul ya farfado sai mutumin yace “a’a kada ka tashi kwanta ka huta dan jikinka akwai rauni garesa” sai Abdul ya koma kwance, sannan mutumin yaje ya samu wasu magunguna ya jikawa Abdul ya kawo ya baiwa Abdul ya sha, sannan kuma ya samu Bandeji ya daurewa Abdul duk inda suka ji masa rauni.
Mutumin nan yayi dawainiya da Abdul sosai kuma ya bashi wasu tufafi ya saka bayan yayi wanka, sannan daga baya ya fahimci Abdul da hankalinsa, haka yasa ya tambayi Abdul yace “Bawan Allah me ya Hadaka da wadannan yara suka biyo ka sunama wannan aiki tareda kiranka Mahaukaci” sai Abdul yayi murmushi yace “Bakomai Bawan Allah, kasan halin kurciya wani abu ne nayi wanda ko mahaukaci bazai iya yi ba amma acikin kuskure na aikata shi, shi ne suka rinka yimin haka” Abdul ya boye wannan sirri ne saboda baya son kowa yasan halin da yake ciki, ba dan komai Abdul baya son kowa ya sani ba, sai dan gudun abashi wata shawara wacce zata danganci yayi hakuri da Mama, sai mutumin yace “to Allah ya kiyaye gaba” “Amin” Abdul ya fada, sai mutumin yace “to amma kabari gobe da safe sai ka tafiyarka, tunda kaga yanzu dare yayi sosai” Abdul ya amince da hakan yayi kwanciyarsa a gidan mutumin...
**** ****
Tun da safe da Baffa yayi sallar Asuba, ko tsayawa karyawa bai yi ba yayi bankwana da mutumin ya tafi. Bayan Baffa ya baro gidan mutumin sai kuma ya dawo kofar gidansu Mama, yana zuwa ya tsaya wurin wata bishiya batare da ya aika kowa kiran Mama ba.
Yana zaune sai ga Mahaifin Mama ya fito zai tafi cikin gari, wurin dube-dubensa sai yaga Baffa, ganin Baffa yayi matukar bashi mamaki dan bai yi tsammanin Baffa zai sake dawowa ba, kuma sai yaga raunuka ajikinsa amma hakan bai hana shi dawowa ba, batare da ya cewa Baffa komai ba ya kada kansa ya tafi, shima kuma Baffa bai cemasa komai saboda gudun fushinsa, shi dai kawai ya zauna ne koda Allah zai sa yaga masoyiyarsa.
Da Yamma Mahaifin Mama ya dawo gida, amma kafin ya shiga ya sake ganin Baffa batare da yace masa komai ba ya shige cikin gida.
Har dare yayi Baffa bai ga Mama ba, sai ya yanke shawarar kwana karkashin bishiyar saboda ba inda ya sani, haka kuwa yayi.
Washe gari mahaifin Mama zai fita ya sake ganin Baffa amma baice masa komai ba ya wucewarsa, da Yamma da ya dawo ya sake ganinsa, wannan karon ma baice masa komai ba ya shige cikin gida. Baffa kuwa mamaki ya ishe shi dan tsawon kwana biyu kenan bai ga koda lekowar Mama garka ba, amma kuma a zuciyarsa bai cire tsammanin ganinta ba, haka yasa ya sake kwanciya anan gindin bishiyar.
Tsawon kwana Hudu Baffa yana wurin ba abinda yake ci sai ruwan da yake sha a wani Fanfo da yake unguwar, ba abinda yake sa ya dauke idonsa ga kofar gidansu Mama sai Sallah amma duk tsawon kwanakin nan bai ga abar kaunarsa ba Mama. Kuma kullum sai mahaifin Mama ya gansa.
Mahaifiyar Mama ta kawo wa Malam abinci wato mahaifin Mama, sai ta zauna, bayan ya kammala cin abinci ya dubeta yace “Mamar Mama kin kuwa san wani abu da yake faruwa?” sai ta dubesa tace “Malam ai sanin abinda yake faruwa sai ku dake fita waje” sai yaci gaba da cewa “Yaron nan wanda Mama ta kafe shi take so, yau tsawon kwana hudu kenan yana bakin garkar nan, duk tsananin abinda nasa yara suka yi masa amma bai hanashi dawowa ba” sai tace “To Malam wallahi ina tausayawa yaran nan, ka dubi yadda suke son junan su, banga abin aibu ba idan kuka bari suka auri junansu ba, ka dubi yarinyar nan yau tsawon kwana shida bata gidan nan mun yi nemanta amma mun rasa duk inda ake tsammanin taje bamu sameta ba, yaron da kake kokarin aura mata yanzu yana can ko ajikinsa babu wata damuwa, amma mu gamu cikin damuwa ko zowa gidan nan ya daina”.
Sai ta numfasa sannan taci gaba da cewa “muna ta zargin ko tana wurin yaron nan, to gashi ashe ba can take ba, ni daman nasan bazata je can ba, dan tasan sai anje nemanta can. To amma Malam me yasa tun farko baka gayamasa bata nan ba” sai Malam yace “saboda shi nakeso ya nemo muna ita, in yaso idan ya dawo muna da ita saina koresa” sai tace “Haba Malam ai wannan daukar alhaki ne, baka tunanin Allah ya tambayeka?” sai yace “ke gafara ke kullum baki ganewa, shin ya za’ayi na baiwa Bahaushe auren ‘ya ta” sai ya tashi tsaye sannan yaci gaba da cewa “Bari na fita nasan yanda zanyi” batare da ya jira amsa ba ya fita waje.
Yana fita waje yaje ya samu Baffa zaune yayi masa sallama, Baffa cikin rawar jikin murnar ganin Mahaifin Mama yazo wurinsa ya amsa sallama, ya durkusa ya gaishe sa, sannan mahaifin Mama ya dubi Baffa yace “Nasan na walakantaka amma kuma hakan baisa kayi fushi damu ba, sannan munyi kokarin rabaku, to amma yanzu nagane lallai idan muka yi haka, to muma zamu dawo nadama, dan haka in dai ni ne na amince da aurenka da Mama” cikin fara’a da murna Baffa yace “Baba nagode sosai, tsawon lokaci kunnuwa basu ji kalma mafi dadin saurare ba irin wannan, ina Mamar take?” sai Mahaifinta yace “Yau tsawon kwana shida Mama tabar gida bamu san inda taje ba, duk inda muke sa ran mu ganta munje amma bamu ganta ba” sai Baffa yayi zaune cikin sanyin jiki, sannan ya dubi mahaifin Mama yace “Baba kada kadamu insha Allahu duk inda Mama take saina nemo ta indai tana duniyar nan” sai yace “bakomai nagode, Allah yabaka sa’a” “Amin” Baffa yace haka, sai mahaifin Mama ya shiga gida.
Bayan ya tafiyarsa sai Baffa ya dawo tunanin inda zai fara neman Mama, gashi Mama ba waya bace da ita ba yanzu, sakamakon mahaifinta ya karbe, gashi shima kuma mahaifinsa ya karbe wayarsa ballai yayi tunanin zata kirasa. Yana cikin wannan tunani sai ya runtse idanuwansa, yana nazarin inda zuciyarsa zata bashi Mama take. Can sai ya bude idanuwansa sakamakon zuciyarsa ta gayamasa inda Mama take.
Kafin Baffa ya tafi yaje gidan bawan Allah nan wanda ya taimakesa lokacin da Yara suke jifansa domin ya samu taimakon kudin mota awurinsa, bayan yaje ya nemeshi taimakon kudin mota cikin nasara ya dauko kudin ya bashi, sai Baffa yayi godiya ya tafi.
Baffa yazo bakin titi ya tare motar zuwa Fakai ya shiga. Bayan sun iso Fakai aka sauke shi ya biya, bai tsaya ko ina ba sai gidan Kawun Mama don nan zuciyarsa ta gayamasa masoyiyarsa taje, yana zuwa ya samu yaro ya tare sai yace dashi “Dan Allah shiga gidan nan kace Baffa na kiran Mama” sai yaron ya shiga cikin gidan ya isarwa mutanen gidan sakon da aka aiko shi, sai yaro ya fito ya sanar da Baffa ya isar da sakon da ya aikesa, Baffa yayi godiya ga yaro, sannan yaron ya tafi.
.
**** ****
Tun da safe Da Abdul yayi sallar Asuba, ko tsayawa karyawa bai yi ba yayi bankwana da mutumin ya tafi.”
“ Bayan Abdul ya baro gidan mutumin sai kuma ya dawo kofar gidansu Mama, yana zuwa ya tsaya wurin wata bishiya batare da ya aika kowa kiran Mama ba.
Yana zaune sai ga Mahaifin Mama ya fito zai tafi cikin gari, wurin dube-dubensa sai yaga Abdul, ganin Abdul yayi matukar bashi mamaki dan bai yi tsammanin Abdul zai sake dawowa ba, kuma sai yaga raunuka ajikinsa amma hakan bai hana shi dawowa ba, batare da ya cewa Abdul komai ba ya kada kansa ya tafi, shima kuma Abdul bai cemasa komai saboda gudun fushinsa, shi dai kawai ya zauna ne koda Allah zai sa yaga masoyiyarsa.”
“Da Yamma Mahaifin Mama ya dawo gida, amma kafin ya shiga ya sake ganin Abdul batare da yace masa komai ba ya shige cikin gida.”
“Har dare yayi Abdul bai ga Mama ba, sai ya yanke shawarar kwana karkashin bishiyar saboda ba inda ya sani, haka kuwa yayi.”
“Washe gari mahaifin Mama zai fita ya sake ganin Abdul amma baice masa komai ba ya wucewarsa, da Yamma da ya dawo ya sake ganinsa, wannan karon ma baice masa komai ba ya shige cikin gida. Abdul kuwa mamaki ya ishe shi dan tsawon kwana biyu kenan bai ga koda lekowar Mama garka ba, amma kuma a zuciyarsa bai cire tsammanin ganinta ba, haka yasa ya sake kwanciya anan gindin bishiyar.”
“Tsawon kwana Hudu Abdul yana wurin ba abinda yake ci sai ruwan da yake sha a wani Fanfo da yake unguwar, ba abinda yake sa ya dauke idonsa ga kofar gidansu Mama sai Sallah amma duk tsawon kwanakin nan bai ga abar kaunarsa ba Mama. Kuma kullum sai mahaifin Mama ya gansa.”
“Mahaifiyar Mama ta kawo wa Malam abinci wato mahaifin Mama, sai ta zauna, bayan ya kammala cin abinci ya dubeta yace “Mamar Mama kin kuwa san wani abu da yake faruwa?” sai ta dubesa tace “Malam ai sanin abinda yake faruwa sai ku dake fita waje” sai yaci gaba da cewa “Yaron nan wanda Mama ta kafe shi take so, yau tsawon kwana hudu kenan yana bakin garkar nan, duk tsananin abinda nasa yara suka yi masa amma bai hanashi dawowa ba” sai tace “To Malam wallahi ina tausayawa yaran nan, ka dubi yadda suke son junan su, banga abin aibu ba idan kuka bari suka auri junansu ba, ka dubi yarinyar nan yau tsawon kwana shida bata gidan nan mun yi nemanta amma mun rasa duk inda ake tsammanin taje bamu sameta ba, yaron da kake kokarin aura mata yanzu yana can ko ajikinsa babu wata damuwa, amma mu gamu cikin damuwa ko zowa gidan nan ya daina”.
Sai ta numfasa sannan taci gaba da cewa “muna ta zargin ko tana wurin yaron nan, to gashi ashe ba can take ba, ni daman nasan bazata je can ba, dan tasan sai anje nemanta can. To amma Malam me yasa tun farko baka gayamasa bata nan ba” sai Malam yace “saboda shi nakeso ya nemo muna ita, in yaso idan ya dawo muna da ita saina koresa” sai tace “Haba Malam ai wannan daukar alhaki ne, baka tunanin Allah ya tambayeka?” sai yace “ke gafara ke kullum baki ganewa, shin ya za’ayi na baiwa Bahaushe auren ‘ya ta” sai ya tashi tsaye sannan yaci gaba da cewa “Bari na fita nasan yanda zanyi” batare da ya jira amsa ba ya fita waje.
Yana fita waje yaje ya samu Abdul zaune yayi masa sallama, Abdul cikin rawar jikin murnar ganin Mahaifin Mama yazo wurinsa ya amsa sallama, ya durkusa ya gaishe sa, sannan mahaifin Mama ya dubi Abdul yace “Nasan na walakantaka amma kuma hakan baisa kayi fushi damu ba, sannan munyi kokarin rabaku, to amma yanzu nagane lallai idan muka yi haka, to muma zamu dawo nadama, dan haka in dai ni ne na amince da aurenka da Mama” cikin fara’a da murna Abdul yace “Baba nagode sosai, tsawon lokaci kunnuwa basu ji kalma mafi dadin saurare ba irin wannan, ina Mamar take?” sai Mahaifinta yace “Yau tsawon kwana shida Mama tabar gida bamu san inda taje ba, duk inda muke sa ran mu ganta munje amma bamu ganta ba” sai Abdul yayi zaune cikin sanyin jiki, sannan ya dubi mahaifin Mama yace “Baba kada kadamu insha Allahu duk inda Mama take saina nemo ta indai tana duniyar nan” sai yace “bakomai nagode, Allah yabaka sa’a” “Amin” Abdul yace haka, sai mahaifin Mama ya shiga gida.”
“Bayan ya tafiyarsa sai Abdul ya dawo tunanin inda zai fara neman Mama, gashi Mama ba waya bace da ita ba yanzu, sakamakon mahaifinta ya karbe, gashi shima kuma mahaifinsa ya karbe wayarsa ballai yayi tunanin zata kirasa. Yana cikin wannan tunani sai ya runtse idanuwansa, yana nazarin inda zuciyarsa zata bashi Mama take. Can sai ya bude idanuwansa sakamakon zuciyarsa ta gayamasa inda Mama take.
Kafin Abdul ya tafi yaje gidan bawan Allah nan wanda ya taimakesa lokacin da Yara suke jifansa domin ya samu taimakon kudin mota awurinsa, bayan yaje ya nemeshi taimakon kudin mota cikin nasara ya dauko kudin ya bashi, sai Abdul yayi godiya ya tafi.”
Abdul yazo bakin titi ya tare motar zuwa garin Fakai nan yake tunanin somota gidan kawunta dake fakai ya shiga motan. Bayan sun iso Fakai aka sauke shi ya biya, bai tsaya ko ina ba sai gidan Kawun Mama don nan zuciyarsa ta gayamasa masoyiyarsa taje, yana zuwa ya samu yaro ya tare sai yace dashi “Dan Allah shiga gidan nan kace Abdul na kiran Mama” sai yaron ya shiga cikin gidan ya isarwa mutanen gidan sakon da aka aiko shi, sai yaro ya fito ya sanar da Abdul ya isar da sakon da ya aikesa, Abdul yayi godiya ga yaro, sannan yaron ya tafi.”
“ Yana tsaye sai ga Kawun Mama ya fito a firgice, yana zuwa Abdul ya durkusa ya gaishe shi, sai Kawunta yace “Kai ne Abdul?” Abdul ya kada kai yace “Eh ni ne Kawu” sai yace “Wallahi tunda Mama tazo gidan nan kwananta biyu tabar gidan bamu san inda taje ba, saboda ana yawan yimata zancen ta hakura da kai” cikin firgita Abdul yace “Kawu nan ma bata nan kenan, Inalillahi wa’inna ilaihir raju’un” sai Kawunta yace “Daman ba gurinka taje ba, dan nasan bazata koma gida saboda dalilinka tabaro gidan” sai Abdul yace “Bata wurina naje gidansu akace kwanan ta shida bata gida, shi ne nazo nan, amma baraz an bincika wani wuri” sai Kawu yace “dan Allah kataimaka ka nemo muna ita bamu san halin da take ciki ba” “Bakomai” Abdul ne yace haka, batare da ya jira Kawunta ya sake cewa wani abu ba, kawai yabar kofar gidan.”
.*
_*Last page*_
**** ****
Bayan ya bar kofar gidan sai kuma ya sake runtse idanuwansa domin nazarin inda zai sake zuwa don ganin Mama, bayan wani dan lokaci ya bude idanuwansa ya doshi cikin wani babban daji, don nan zuciyarsa tabasa masoyiyarsa Mama tana nan.”
Yayi tafiya mai nisa acikin daji gashi yunwa da kishirwa na damunsa amma bai hangi kowa ba acikin jinsin mutane ballai ya nemi taimakon koda ruwan sha ne. Can yana tafiya yakara yin nisa sosai cikin daji sai ya hango wasu mafarauta sun zagaye wata yarinya, tun yana nesa ya hango su, bai tsaya bata lokaci ba ya karasa inda suke, yana zuwa koda ya kalli yarinyar dake tsakiyar sai yaga Mama dinsa ce, cikin karfin hali yayi sauri ya tsallaka tsakiyarsu ya isa wurin masoyiyarsa, Mama na ganinsa tayi wata irin murna wacce ta jima bata yi irinta ba, sai daya daga cikin,mafarautan yace “kai wanene kai da zaka shigo tsakiyar mu muna kan aiki” Abdul bai samu damar mayar masa amsar tambayarsa ba saboda tunda ya fado tsakiyarsu kallon Mama kawai yake har ya manta da akwai wasu akusa dasu.”
“Cikin yana yin fushi dayan Mafarautan yakai masa duka wanda yayi sanadiyar faduwar Abdul kasa, Abdul yana kasa ya dubesu cikin mamaki yace “ku kuwa su waye da kuka zagaye masoyita, me kuke so” sai suka amsa masa da cewa “ita muke so mu tafi da ita” cikin dariya Abdul ya tashi ya kakkabe jikinsa yace “au daman akwai wanda duniya zai iya daukar masoyiyata daga gareni, daman akwai wanda zai iya tabin jikin masoyiyata agabana, wallahi duk wanda yayi yunkurin tabin masoyiyata sai yayi nadama, abu mafi sauki ku tafi kawai kubarmu da abinda ya ishe mu” sai Babbansu yace “Lallai yaron nan ka raina mu, to bara ka gani” sai yaje da niyar rike hannun Mama, da hanzari Abdul yazo wurinsa yakai masa naushi wanda yakaisa kasa, sai saura suka farma Abdul daganan suka cigaba da fafatawa, cikin ikon Allah Abdul ya samu damar dokesu su duka, da suka ga alamun babu riba suka ruga da gudu suka bar Abdul tareda Mama.”
Bayan sun gudu, sai Abdul ya dubi Mama yana shesshekar gajiya yace da ita “Ke kuwa me ya kawo ki wannan gungurumin daji?” sai Mama tayi murmushi tace “Ni ne da mamaki ba kai ba, ya akayi kasan ina wannan dajin?” sai Abdul yayi murmushi yace “shin kesan cewa koda yaushe zuciyoyin mu suna tare gangar jikin mu kadai ne a rabe, aduk lokacin da na runtse idanuwana nakan ganki acikinsu da kuma yanayin da kike, sannan idan ina bukatar sanin inda kike zuciyata ita take gayamin inda ‘yar uwarta take ma’ana inda kike, nakan bi dukkanin inda lumfashin zuciyata yake bugawa dan na tabbata kina wurin, kuma sai yanzu nakara tabbatar da hakan, tunda ta gayamin nazo nan kuma nazo na sameki” sai Mama tasake yin murmushi a karo na biyu, sannan tace “tun lokacin da nabaro garinku, na dawo gida amma nakasa zama, shiyasa naje wurare da dama amma duk inda na zauna aka tambayan matsalata nakan fada, amma kowa abinda yake gayamin nayi hakuri dakai, ni kuma nagaji da jin wannan mummunar kalma, shiyasa nayi nesa da mutane, dan nahuta dajin wannan mummunanr kalma, wannan wurin da nake yana debemin kewa saboda soyayyarka ita kadai ce abar hirata, tunaninka kuwa shi ne abinci na, nazarin kalamanka su suke debemin kewa” sai yayi murmushi yace “to albishirin?” “Goro” Mama ce amsa haka tana cike da fara’a, sai Abdul yaci gaba da cewa “Mahaifinki ya amince da auren mu, shi ne ma yabani damar nemoki, dan haka mu hanzarta mu koma gida” Mama tana murna ta dauko mayafinta ta daurewa Abdul rauninda mafarautan nan suka yi masa abaya, suka kama hanyar zuwa gida.”
Bayan doguwar tafiyar da suka yi acikin daji har suka iso gida, suna zuwa Kawunta ya gansu ya kuma yi murna sosai tareda jinjinawa Abdul, sai kuma matarsa ta dauko mayafi ta baiwa Mama, sannan Kawu ya shiryo dan biyo su Mama gida tare. Sun je tashar mota sun shiga motar zuwa Kano cikin sa’a basu jima ba mota ta cika suka kama hanyar Kano."
”Bayan sun iso Kano suka zo gida, suna isa cikin gida mahaifin Mama ya tarbesu cikin fara’a, mahaifiyarta ta rugo ta rungume Mama, sai Mahaifin Mama ya dubi Abdul sannan ya dubi kanensa, sai ya cewa Abdul “Mun gode sosai Abdul Allah ya biyaka kuma naso na baka auren Mama amma kuma sai gashi wata kaddara ta gifta?” cikin tsananin mamaki Mama ta saki mahaifiyarta ta dubi babanta tace “Baba wace irin kaddara kuma” sai ya kalleta yace “Kin fi kowa sanin bama baiwa duk wanda yaji rauni a bayansa auren ‘ya’yan mu kuma gashi Abdul yaji rauni agurin” Mama tana kuka tace “Baba wannan al’ada ai ba daga wurin Allah ta fito ba, sannan katuna awurin cetona ya samu wannan rauni” Abdul na tsaye sai jiri yake ya kasa cewa komai saboda tsananin mamaki, sai Mahaifinta yace “Nadai gaya miki” Mama bata kara cewa komai ba, taje ta nemo wuka ta yanka a bayanta, cikin Firgita Babanta yace “Mama miye haka, kin yi haukane kike yankawa kanki wuka” Mama na hawaye tace “Baba a wannan lokaci wallahi zan iya aikata abinda mahaukaci bazai aikata ba, na yankawa kaina wuka abaya ne saboda nima nayi irin raunin da Abdul yayi, idan kuma hakan baisa kuka amince da auren mu ba, wallahi saina kashe kaina” a lokacin Kawunta yace “Yaya kawai ka amince da aurensu in har ba so kake muyi hasararta gaba daya ba, na tabbata a yadda take ji a zuciyarta zata aikata abinda tace” sai kuma Abdul yace “Mama kada ki aikata hakan, ki bi umarnin iyayenki mu hakura da juna indai basa son auren mu” sai Mama tace “Wallahi bazan iya hakuri da kai ba koda kai zaka iya hakuri dani, kuma yanzu zan aikata abinda nace”.
Sai Mahaifinta yayi sauri yace “Mama ajiye wukar na amince ki auri Abdul, kada ki aikata wannan mummunan zunubi, bazan yi sanadin fadawar ‘yata cikin wutar jahannama ba, na amince” sai Mama tace “sai kayimin alkawari sannan zan ajiye” sai mahaifiyarta tace “Ki ajiye Mama basai yayi miki alkawari ba, nasan ya amince har azuciyarsa” sai Babanta yace “Nayi miki alkawari na amince da aurenku” sai Mama ta ajiye wukar ta rungume Mahaifiyarta.”
“Bayan amincewar Mahaifin Mama, sai kuma ya umarci Abdul suje dashi da Mamar da kuma kanensa, dan ya baiwa mahaifinsa hakurin abinda ya aikata musu, tareda rokonsa shima ya amince.
Sun shigo mota su hudu sun hawo hanyar Bauchi, Abdul da Mama murna kawai suke a zuciyarsu amma sai suka boye basu bayyana a fuskarsu ba, amma kuma da kagansu kasan akwai farin ciki atattare dasu.”
“Allah ya kawo su garin Bauchi
lafiya, sannan suka je gidansu Abdul, inda suka tarar da mahaifin Abdul yana batun fita, da sauri Abdul yaje ya durkusa gaban mahaifinsa yana kuka yace “Dan Allah Abba ka gafartamin laifina dana aikata muku wallahi banida zabi akan hakan ne” sai kuma yaje gaban Mamarsa yace “Hajiya dan Allah ku gafartamin” yana cikin kukan ne Hajiya ta riko hannunsa ta tasuwa shi tsaye batare da tace komai ba, itama ta dinga zubar da hawaye. Sai kuma mahaifin Mama yazo wurin Alhaji yace “Alhaji kayi hakurin abinda muka aikata, cikin rashin sani ne da sharrin shaidan, mun dade muna kyamar aurar da ‘ya’yan mu ga Hausawa, sai yanzu ‘ya’yan mu suka fahimtar damu wani abu wanda muka dade bamu fahimta ba, ashe shi SO babu ruwansa da Yare, sannan Allah yakan hada kauna tsakanin duk wadan da yaso, dan haka ina mai nemanka gafara ka yafemin abinda na aikata maka, na amince kuma inason kaima ka amince, ta yuyu ta wannan hanyarce zamu samu magance nuna banbancin Yare, sannan mu sakawa wadannan yara albarka shi ne alkhairi agaremu bamu yi kokarin rabasu ba” sai Alhaji ya dubi Mahaifin Mama yace “Babu komai, komai ya wuce Allah yakara ganar damu, a baya harna yanke shawarar ko ka amince ni bazan amince ba, amma yanzu ba abinda zance bayan Allah yasa ayi damu, sannan Allah ya albarkaci aurensu” sai kowa dake wurin yayi murna, musamman su Abdul da Mama.”
“Soyayyar Abdul da Mama ta dawo cikin farin ciki da jin dadi batare da wani shamaki ko fargaba ba, daman ita rayuwa mai hakuri yake da nasara, sannan kuma soyayya abu ce mai daraja wacce take da wuyar samu cikin sauki, haka zalika duk tsanani sauki yana nan zuwa. Yanzu gashi iyayensu sun amince da auren su wanda basu yi tsammanin samun wannan nasarar ba a baya, amma da yake komai na Allah ne gashi yanzu sun cimma nasara.”
“An saka ranar auren Mama da Abdul an yi komai da ake na aure kamar su, Lefe kudin Sadaki komai anyi har an saka rana.
Ranar Aure anyi biki cikin farin ciki da jin dadi, sannan an yi shi abin burgewa, an je Kano an daura auren Abdul da Mama,.”
“Da daddare abokan Ango su Usman da Bashir da Ibrahim da Mansur da dai sauransu sun kai abokinsu Ango wato Abdul dakin Amaryarsa wacce aka kawo masa tun sallar Isha’I da yake ba gari daya bane wato Mama. Sun yiwa Ango da Amarya huduba harma da zolayar da abokan Ango suke idan sun kawo Ango duk anyi suka tafi suka bar Ango da Amarya acikin daki su kadai.”
“Sun je sun yi Sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, sun zo sun zauna suka fara hirarsu, acikin hirar Mama ta kalli Angonta Abdul tace “Angona ashe daman zamu ga wannan rana a rayuwarmu?” cikin murmushi Abdul yace “Amaryata kenan, aini daman ban taba cire tsammanin ganin wannan ranar ba, saboda bana tunanin akwai wanda zai iya rabamu a duniyar nan in ba Allah ba” sai Mama ta lumshe ido cikin shagabawa tace “Hmm kaida kace ka yafe ni” “Wa! Hmm ai kawai fada ne nayi a baki amma ba haka bane a zuciyata ba, ya za’ayi na yafe wacce na sallamawa dukkanin lamarina, wacce kullum mafarkina itace, wacce zuciyata batasan kowa ba sai ita, ai ni dake babu mai rabamu” Abdul ne yace haka, sai Mama tace “to Allah yabarmu tare, sannan ya albarkaci rayuwarmu ya bamu zuri’a dayyiba” sai yace “Amin Amaryata shalelena” sai suka tashi domin kwanciya, a Daren ranar Abdul ya karbi hakkinsa wajen Mama Tasha wuya hannun Abdul shikuma sai faman zubamata Rowan, albarka yake, ya gasamata jiki bayan sunyi wanka suka haye gado rungume da juna haka bacci ya debesu.”
“Rayuwar auren Abdul da Mama ta kasance cikin farin ciki da jin dadi, don kuwa babu wanda ya taba jin kansu, shima kuma Usman ya samu wurin cin abinci koda yaushe, dan kullum acan yake zuwa yana kwasar girki ya huta da karbar bashin garin kwaki.
"BAYAN WATA HUDU"
“bayan wata hudu Allah ya azirtasu da samin ciki sosai sukayi murna kula na mussamman Mama ke samun wajen mijinta da dangi.”
."Ciki Nada 9mnth ta haiho yan biyu duka maza, basai mun tsaya fadamuku farincikin da zasuyiba just imagine readers."
"Ranar suna yara suka ci sunansu Anwar da a
Ammar, anyi shagali har mun hangosu xarah bukar, Yar Ficika, walliya,Maryam G,Anker, Belly badaru, asy Khallel,RAZ,da sauransu sunata kwasan rengem, bamubar su Mr smile, ililee, raheem jegs anyi shagali lpy an watse."
“haka rayuwa taci gaba da tfy cikin jin dadi dakwanciyar hankali,yara suna girma suna kyau da wayo, Abdul yasami Karin girma a wajen aiki komai yana tafiya dadai ALHAMDULILLAH..... Muna wa Abdul da Mama fatan alheri a rayuwarsu Allah yasa mu dace ameen....
TAMMAT BI HAMDILLAHI….
0 Comments:
Post a Comment