Barcelona zata siyo Ighalo dan ya maye mata gurbin Suarez
Shahararriyar Kungiyar kwallon kafa ta kasar Sifaniya Barcelona ta fara duba yiyuwar sayen dan wasan Najeriya dake bugawa kungiyar Changchun Yatai ta kasar China wasa, Odion Ighalo dan ya zamar mata wanda zata rika canja dan wasanta Suarez dashi.
Barca na neman Ighalone tsohon dan wasan Watford saboda me ci mata kwallo Suarez na daf da daina buga wasa sannan kuma Munir zai bar kungiyar zuwa karshen watannan, hadi da cewa basu so su kashe kudi da yawa wajan sayen sabon dan wasa wanda zasu rika canjashi da Suarez yanda shi Suarez din zai zama sai idan za'a buga babban wasane zasu rika sakashi.
Sport ta ruwaito cewa, Barca ta dade tana bibiyar Ighalo amma bata fito da maitarta fili ba sai yanzu.
Shidai Suarez ya bayyana yanda yake ji da neman madadinshi da Barca take bayan da yaci kwallaye uku a wasan da suka buga da Real Madrid wanda ya kare Barca na cin Madrid 5-1 a watan Octoba na shekarar 2018 da ta gabata inda yace, yana farin ciki da kwallayen da yaci amma fa Barca basu nuna mai cewa yana daya daga cikin fitattun masu cin kwallo na Duniya ba.
Ya kara da cewa ya fahimci neman madadinshi da suke saboda yanzu shekarunshi 31.
Ighalo dai yayi bakin jini ga 'yan Najeriya a wasan da Najeriyar ta buga da kasar Argentina a gasar cin kofin Duniya na shekarar 2018 da aka buga a kasar Rasha saboda damarmakin daya barar.
Sunday, 13 January 2019
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon shekarar 2018Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon shek
Messi da Suarez sun ci kwallaye fiye da na Madrid Messi da Suarez sun ci kwallaye fiye da na Madrid
De Gea ya cire wa Manchester United kitse a wutaDe Gea ya cire wa Manchester United kitse a wutaM
Ana Cigaba Da Nunawa Dan Wasa Yerry Mina Wariyar Launin FataEverton tana aiki tare da hukumar da takeyaki da
Kalli hoton Anthony Joshua da Cristiano Ronaldo da ya dauki hankulaKalli hoton Anthony Joshua da Cristiano Ronaldo d
City ta ci gaba da kankane teburin PremierManchester City ta je ta doke Watford 2-1 a wasan
0 Comments:
Post a Comment