De Gea ya cire wa Manchester United kitse a wuta
Mai horar da Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya jinjina wa mai tsaren ragarsu, David De Gea bisa gagarumar rawar da ya taka a nasarar da suka samu kan Tottenham a gasar firmiyar Ingila, in da suka tashi 1-0.
Solskjaer da ke zama kocin rikon kwarya a kungiyar ya bayyana, De Gea a matsayin gola mafi kwarewa a duk fadin duniya, yayin da ya ce, golan na kokarin kafa tarihin da za a ci gaba da tunawa da shi a Manchester United.
Mai tsaren ragar ya kauwar da kwallayen da dama da Tottenham ta kai hare-harensu musamman bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Marcus Rashford ne ya jefa kwallon daya tilo a fafatawar ta ranar Lahadi.
Gabanin Solskjaer ya karbi aikin horar da Manchester Unted, akwai tazarar maki 8 tsakaninta da Arsenal, amma a yanzu kungiyar ta kulle wannan tazarar, in da kowacce daga cikinsu ke da maki 41.
Kocin ya samu nasara a dukkanin wasanni shida da ya jagoranci kungiyar tun bayan maye gurbin Jose Mourinho a cikin watan Disamba.
Ita ma Everton ta samu nasara akan Bournmouth da ci 2-0 a karawar da suka yi a gasar ta firimiyar Ingila, abin da ya ba ta damar darawa mataki na 10 a teburi.
RFIhausa.
Monday, 14 January 2019
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
Solksjaer ba shi da farin ciki da Fellaini, zai iya buga wasan tsakiya a JanairuSolksjaer ba shi da farin ciki da Fellaini, zai i
Messi ne kan gaba a kwallaye a Turai Messi ne kan gaba a kwallaye a Turai Dan wasan t
CAF ta kwace gasar kwallon kafa daga wurin Kamaru[post by samaila umar lameedo]CAF ta kwace gasar
Barcelona zata siyo Ighalo dan ya maye mata gurbin SuarezBarcelona zata siyo Ighalo dan ya maye mata gurbi
Messi ya zama dan kwallo na farko da ya ci kwallaye 400 a La LigaMessi ya zama dan kwallo na farko da ya ci kwalla
Dan wasan Tottenham Kirista Eriksen yana son komawa Real MadridDan wasan Tottenham Kirista Eriksen yana son koma
0 Comments:
Post a Comment