Sunday 20 January 2019




Gwamnatin ganduje ne ta fara kammala ayyukan da ta gada

Home Gwamnatin ganduje ne ta fara kammala ayyukan da ta gada

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Gwamnatin mai girma Dakta Abdullahi
Umar Ganduje OFR ta kammala aikin ginin gadar saman kan titin Murtala Muhammad (Sabon Gari) wadda ta gada a lokacin da aikin gininta bai wuce kashi 25 cikin dari (25%) ba. A yanzu abin da ya yi saura kawai shi ne taron bude ta. Ba makawa wannan gadar saman za ta saukaka zirga-zirga da rage tsawon lokacin tafiya daga bangare daya na birnin zuwa dayan bangaren.
Babu wata gwamnatin jiha a Nijeriya da ta kammala manyan ayyukan da ta gada daga wasu gwamnatocin da kuma wasu sababbin ayyukan daban kamar Kano, kuma karkashin shugabancin Ganduje. Saboda haka, ba makawa Ganduje ya cancanci ya zarce domin ya cigaba da kaddamar da tarin ire-iren wadannan ayyukan masu kayatarwa da ban mamaki.








Share this


Author: verified_user

0 Comments: