"Babu wanda ya fi karfin doka kuma duk mukaminsa sai mun hukunta shi, don doka gaba take da kowa", in ji kwamishinan 'yan sanda na jihar Wakili Mohammed.
"Babu yadda za a yi a ce wasu tsuraru su ji sun fi karfin doka.
"Don haka mun hana yawo da kowane irin makami, kuma mun hana fita da 'yan banga yawon yakin neman zabe." inji Wakili.
Har wa yau, ya kuma ce rundunar 'yan sandan jihar za ta sanya kafar wando daya da masu sayar da kwaya da kayan maye a jihar. Wakili Mohammed ya ja hankalin iyaye da su ja kunnen 'ya'yansu kan shiga bangar siyasa don guje wa fushin hukuma.
Yanayin siyasa a jihar Kano na kara munana duk da yarjejeniyar da yan takara suka sanya wa hannu kan yakin neman zabe da gudanar da zaben cikin lumana a jihar.
A ranar Lahadi ne 'yan daba suka rika far wa mutane tare da yi masu kwace jim kadan bayan ziyarar da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya kai jihar Kano domin yakin neman zabe.
0 Comments:
Post a Comment