Thursday 7 March 2019




KAR KU YADDA A RUDE KU DA BATUN BIDIYON GANDUJE

Home KAR KU YADDA A RUDE KU DA BATUN BIDIYON GANDUJE

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Don Allah kowa ya daure ya karanta wannan rubutun har karshe, kafin a bayyana ra'ayi ko fahimta, banda zagi da cin mutuncin juna.
Bayan na gama tattara dalilai na 'yan adawa da suke sukar Maigirma Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da shi, gaba daya abin da suke sukarshi a kai bai wuce batun wani faifan bidiyon zargi wanda 'dan jaridarsu ya fitar ba.
Wannan ne dalilin da yasa na yanke shawarar shiga rigar 'yan sanda masu binciken manyan laifuka domin na warware mana tsakanin zare da abawa akan bidiyo na zargi irin wannan da 'dan jarida ya fitar akan Gwamna Ganduje, zanyi cikakken bayani a bisa mizanin ka'idoji na bincike.
Idan aka dauki bidiyon 'dan jaridar 'yan adawan Gwamna sai aka aza akan ka'idar "Forensic analysis" to a gaskiya babu alaka tsakanin wannan bidiyo na zargi da shi Maigirma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ko da kuwa bidiyon na gaskiya ne ba a na'ura mai kwakwalwa aka tsarashi ba, kamar yadda 'yan ta'adda suke zama a cikin daki su tsara bidiyon farfaganda.
Dalilin da yasa nace babu alaka tsakanin wannan bidiyon zargi da shi Maigirma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shine idan akaje yanke hukunci a gaban alkali akwai wasu abubuwa na gaskiya (fact ingredients) da suke kan doron doka da dole sai sun shiga cikin bidiyon kafin a yarda da alakarsa da Maigirma Gwamna Ganduje.
Idan akace "wanda ake zargi da aikata laifi" (crime suspect) to sai an hada abubuwa da dama kafin a yarda a amince da cewa an aikata laifi, misali:-
Waye ya aikata laifin (suspect)?
A ina aka aikata laifin (scene of crime)?
Wanda aka aikatawa laifin (victim)
Shaida sahihiya (factual evidence)
Dole sai wadannan abubuwa sun hadu kafin a tabbatar da an aikata laifi jama'a a dokar Nigeria kuma kusan haka yake a dokar musulunci.
Musamman ita shaida sahihiya itace alkali ke dogaro da ita ya tabbatar da an aikata laifi, misali:-
-Ina shaidar Gwamna Ganduje ya karbi kudin cin hanci? amsa shine ga bidiyo da 'dan jarida ya fitar amma watakila ba kudin cin hanci bane yake karba sakone ko kuma tallafi ne aka bashi
-Shin bidiyon sahihi ne? amsa babu tabbacin haka domin har an saka wakar sharewa a cikin bidiyon
-Waye ya mika kudin da ake zargi na cin hanci ne? amsa babu, kuma ba'a sanshi ba, ba'a nuna fuskarsa ba
Wadannan abubuwa ne da dole sai an tabbatar da gaskiyarsu a matsayin shaida kafin ace Gwamna ya aikata laifin karban cin hanci, wannan ka'ida na karban shaida sahihiya shine abinda alkalan musulunci suke cewa "Qarina mu'allaqah" a turance "circumstantial evidence"
A ka'idar tattara shaida sahihiya, akwai abinda ake kira da gurbacewa ko gurbatacciyar shaida (contamination of evidence), ita wannan gurbacewar shaida tana faruwa ne duk lokacin da akace ga sahihiyar shaida, sai akace an kara wani abu akan shaidar, ko kuma an rage wani abu akan shaidar, musamman shaida da ake nema na abinda ya shafi alaka da na'ura mai kwakwalwa ko laifukan yanar gizo (Cyber crimes), da zaran an samu kari ko ragi to shaida ta lalace jama'a.
Saboda haka ku lura a farkon bidiyon da 'dan jaridar 'yan adawa ya fitar na zargin Maigirma Gwamna na karban cin hanci sai akaji wata karar sharewa na tashi a cikin bidiyon, wannan ya nuna cewa anyi editing bidiyon aka kara wani abu, don haka shaidar gaskiyan bidiyon ko da sahihi ne to ya lalace a ka'idah.
Ya ku jama'ar Kano kar ku yarda a rudeku da wannan bidiyo wanda 'dan jaridar 'yan adawa ya fitar don cimma burin su na siyasa, a rubutun da nayi a baya na fada muku cewa 'yan adawa da suka tashi fitar da bidiyon (wanda ni dai ban yarda da sahihancinsa ba) sai sukayi amfani da 'dan jaridarsu saboda su samu kariya na dokokin aikin jarida ko da ya tabba karyane da sharri da batanci to ba zai fuskanci hukunci mai tsanani a gaban alkali ba, iyakaci yayi rubutun bayar da hakuri yace an samu kuskuren aikin jarida, shikenan magana ya kare.
Kanawa kar ku yarda a raba tsakaninku da gwamna Abdullahi Umar mai kokarin kwatanta gaskiya da adalci, mai halin dattako wanda ya dauko hanyar gina sabuwar jihar Kano, kar ku yarda a rabaku dashi, idan Allah Ya kaimh ranar asabar ku fito ku bashi kuri'ah don ya zarce.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: