A yanzu dai, marar lafiyan da ke zaune a birnin Landan ya daina nuna alamun cutar tsawon wata 18 kuma ya daina shan magungunan cutar.
Sai dai masu bincike na ganin cewa akwai sauran lokaci kafin a ce marar lafiyan ya warke gaba daya.
Masana dai na ganin wannan wani mataki ne mai muhimmanci a gano maganin cutar AIDS.
Wasu masana ne daga Jami'o'in Landan da Imperial da Cambridge da kuma Oxford suka hada kai wajen yin wannan aikin.
Wannan ne karo na biyu da wani mai dauke da cutar ya warke ta wannan hanyar.
Shekaru goma da suka wuce, aka yi wa wani mai dauke da cutar dashen bargo daga wani wanda ba ya dauke da cutar.
Sinadarin CCR5 shi ne ke bai wa kwayar cutar HIV damar shiga cikin kwayoyin halittar dan Adam.
Sai dai akwai 'yan tsirarun mutane a duniya da ba sa iya kamuwa da cutar AIDS saboda ba a halicce su da sinadarin CCR5 din ba.
Ana yi wa mai dauke da cutar HIV dashen kwayoyin halitta daga mutumin da ba ya dauke da sinadarin CCR5.
An yi wa marar lafiyan na Landan dashen kwayoyin halitta daga jikin daya daga cikin irin mutanen da ba su da CCR5 kuma daga nan sai jikinsa ya gaza daukar kwayar cutar HIV din.
Sai dai ana iya samun kwayoyin cutar HIV din kadan a jikin sai dai ba za su yi wani tasiri ba.
0 Comments:
Post a Comment