Tuesday 5 March 2019




Kotu Ta Soke Duk Wasu Tuhume-Tuhumen Da Take Wa Marigayi Alex Badeh

Home Kotu Ta Soke Duk Wasu Tuhume-Tuhumen Da Take Wa Marigayi Alex Badeh

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Babbar Kotun Tarayya Reshen Abuja, ta soke dukkan tuhume-tuhumen badakalar wawurar kudade da EFCC ke yi wa tsohon Ministan Tsaro, marigayi Alex Badeh.
Wasu ‘yan bindiga ne suka bindige Badeh a cikin shekarar da ta gabata, a kan hanyar sa bayan ya dawo daga gonar sa a jihar Nassarawa.
Babban Mai Shari’a Okon Abang ya soke karar da tuhume-tuhumen a cikin hukuncin da ya bayar, wanda aka samu kamfanin Badeh mai suna Iyalikam Nigeria Limited da shi Badeh din kan sa da aikata laifukan da aka caje shi.
Ana tuhumar sa ne da laifuka 10 da suka jibinci wawurar kudaden makamai a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan.
Kotu ta umarci cewa dukkangidajen da aka samu a hannun Badeh, a mallaka su ga gwamnatin tarayya ta hannun EFCC.
Mai Shari’a ya kuma ci gaba da cewa a shaida wa Hukumar Rajistar Masana’antu da Kamfanoni ta Kasa wannan hukunci da kotun ta yanke.
“Tunda ya amsa laifin sa, kuma ya amayar da abin da aka amince zai amayar din, to na yanke hukuncin cewa an kama shi da laifi.
“Tunda kuma wanda ake tuhumar ya rigaya ya musu bayan ya amsa laifin sa, kuma ya amince zai maido kadarorin, to daya yau an soke kuma na kashe dukkantuhume-tuhumen da kotu ke yi masa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: