Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Muhammad Yayi Sanarwa.
Labarin da muke kawo muku kai tsaye daga fadar mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Abubaakar Sa'ad na nuna cewa an ga sabuwar jaririyar watar Shawwal, a yau Litinin 29 ga watan Ramadan wanda yayi daidai da 3 ga watan Yuni, 2019.
Sarkin Musulmi ya sanar da cewa gobe, ranar Talata ce 1 ga watan Shawwal kuma Sallar Idi
Yace: Bisa ga shari'ar Musulmi, muna masu sanar muku da cewa a yau Litinin 3 ga watan Yuni 2019 wanda yayi daidai da 29 ga watan Ramadan 1440, ne karshen watan Ramadana na shekarar 1440AH."
"Mun samu rahotannin tabbacin ganin wata daga shugabannin adinin Musulunci daga gari daban-daban.. Mai martaba Shehun Borno, Sarkin Gwandu, Sarkin Jema'a, Sarkin Damaturu, da wasu sa sassan jihar sokoto
Bisa da haka, gobe Talata 4 ga watan Yuni, 2019 ta zama 1 ga watan Shawwal 1440AH kuma ranar Sallah. Muna rokon Allah ya karba ibadun da mukayi a cikin watar Ramadan."
Source: Legit
Tuesday, 4 June 2019
Author: Anonymous verified_user
RELATED STORIES
House of Reps ya ci gaba da karantawa na biyu na
Sambo Dasuki Na Nan A Raye Bai Mutu Ba, Cewar Hukumar DSSHukumar tsaro ta farin kaya, DSS ta karyata labar
Kamfanin dillancin labaran na NLC ya bayyana a Oyo akan albashin da ba a biya ba, matsalolin gabatarwaKamfanin dillancin labaran na NLC ya bayyana a Oy
Littafin Mijin Ummata Kashi Na Sha Daya Zuwa Na Sha Biyar😍📚 MIJIN UMMATA littafi Na SHADAYA 😘📖% Bayan
An Kama Mutum 50 Kan Rikicin Siyasar Jihar KanoRundunar 'yan sanda ta jihar Kano a Najeriya ta c
Shugaba muhammadu buhari ya bayyana wasu jahohi mafi kaskanci a Nigeria. Shugaba muhammadu buhari ya bayyana wasu jahohi m
0 Comments:
Post a Comment