Tuesday 4 June 2019




Rikici ya barke tsakanin Fati Muhammed da Teema Makamashi akan soyayyar Sanata Dino Melaye.

Home Rikici ya barke tsakanin Fati Muhammed da Teema Makamashi akan soyayyar Sanata Dino Melaye.

Anonymous

Ku Tura A Social Media
Rikici ya barke tsakanin Fati Muhammed da Teema Makamashi akan soyayyar Sanata Dino Melaye.

An dai ga Teema Makamashi tana habaici a shafinta na Instagram inda
Duka 'yan matan sun yiwa Sanatan waka da fasta ta siyasa sun kai masa, inda ya dauki hoto da kowaccen su
Wani rikici da ya barke tsakanin matan Kannywood guda biyu Teema Makamashi da Fati Mohammed, inda suke rikici akan Sanatan jihar Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye.
Rikicin ya samo asali ne lokacin da Teema Makamashi take gargadin Fati Mohammed akan kwaikwayenta da tayi wurin yiwa Sanatan waka.
Ga abinda Teema Makamashi ta rubuta a shafinta na Instagram:
"Keda samun soyayyarsa sai dai ki gani daga nesa"
Tauraruwar Teema Makamashi wacce ita ce ta fara yiwa Sanata Dino Melaye waka, tayi wannan habaicin ne ga Fati Mohammed wacce ta kwafeta.
Teema tayi rubutun ne a shafinta na Instagram inda ta cigaba da cewa, "Ga wani sabon salon shima idan zaki yi, banda waka, tunda kome nayi sai kinyi, kina tare da bakar wahala indai ni zaki dinga kwaikwaya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: