Tauraron me fadakarwa a shafin sada zumunta na Twitter, Mustafa da aka fi sani da Angry Ustaz ya bayar da labarin yanda wata Amarya bayan daura auren ta da angonta, ana shirin kaita gidan mijin nata sai ta rasu.
Yace, wata budurwa a garin Maiduguri da aka wa aure jiya, kawayenta sunzo da yamma, wajan karfe takwas dan rakata gidan mijinta, sai tace tana jin ciwon kai, daya daga cikin kawayen nata tace tadan kwanta, kwanciyar da bata tashi ba kenan, rai yayi halinshi.
Ustaz ya kar da cewa, wane irin tanadi mukawa mutuwa, mun shirya?.
0 Comments:
Post a Comment