Matashin dai ya rubuta cewa "Karshen su yazo yau (watau Hausawa da Fulani), gamu nan muna ta kashe Hausawa da Fulani a garin Kunini kamar awaki".
NAIJ.com ta samu cewa irin wadannan kalaman na nuna kiyayya na zaman tamkar wasu guma-guman dake rura wutar rikicin kabilanci a yankunan jahohin Arewa ta tsakiya irin su Taraba din.
Tuni dai jama'a da dama da suka ga rubutun na matashin suka yi Allah-wadai da shi tare da jan hankali da kira ga jami'an tsaro da su tabbatar da doka ta hau kan matashin domin hakan ya zama izina ga 'yan baya.
Abun zura ido agani yanzu dai shine ko jami'an tsaro za su farka daga baccin da suke yi domin ganin doka tayi aiki akan matashin da ma sauran masu irin tunani da halayyar sa a ko'ina suke a fadin kasar.
0 Comments:
Post a Comment