Wani hazikin karamin yaro dan kasar Amurka me suna Emette Brewster yayi kutse a kwamfutar gwaji irin ta zaben kasar Amurka sannan ya canja sakamakon zaben cikin mintunan da basu wuce 10 ba.
Yaron yayi wanan bajintane a lokacin taron DEFCON da ake shiryawa a kasar ta Amurka inda ake tattara gwanaye a harkar kwamfuta a basu na'urorin gwaji dan su yi kokarin kutse a cikinsu.
A wannan karin, taron ya shigo da kananan yara cikinshi inda aka basu irin wannan dama, aikuwa basu yi wata-wata ba suka yi ta bada mamaki, wanda yafi daukar hankali shine na wannan yaro me suna Emette, kamar yanda jaridar Times ta ruwaito.
Tuni dai har yaron ya fara samun yabo da kira da a daukeshi aikin samarwa da kwamfutoci tsaro a kasar.
0 Comments:
Post a Comment