Ana ci gaba da samun yawan mace-mace na matasa maza da mata masu ban al’ajabi a kullun.
Hakan ce ta kansance ga wata kyakyawar matashiya, Aisha Ahmed, wacce aka sanar da mutuwarta watanni uku bayan aurenta. Ta rasu ne bayan yar gajeriyar rashin lafiya.
A cewar daya daga cikin, kawayen ta, marigayiya Aisha da mijinta sun yi aure ne a ranar 28 ga watan Afrilu sannan ta rasu a ranar AAsabar, 7 ga watan Yuli.
Kawarta Aisha Salisu (@aishasalisu63), ta wallafa hotunan marigayiyar da dama a shafinta na Instagram yayinda ya yi wasu zantuka masu taba zuciya.
Ga hotunan a kasa:
0 Comments:
Post a Comment