Tuesday 6 July 2021

SADIO MANE YAYI BAYANI MAI MATUQAR JAN HANKALI..

SADIO MANE YAYI BAYANI MAI MATUQAR JAN HANKALI..

Sadio mane dan wasan kungiyar kwallon kafa ta liverpool dake england kuma haifaffen kasar SANEGAL,,,Cikin bayanin da yafitar shahararren Dan wasan gaba a qungiyar kwallon kafa ta Liverpool dake kasar England, 
Dan wasan yayi bayanin cewar baya daga cikin tsarinsa na siyan motoci masu tsada ko manyan wayoyin hannu, a'a shidai burin Dan wasan shine ganin cewar yan uwasan dake kasarsa sunkwanta adakunansu cikin nutsuwa da kwanciyar hankalin bayan sunci abinci.
 Haka zalika basu da shayin zuwa asibitoci Dan Neman magani. Bugu da qari Dan wasan yace yanason ganin fanni. Koyo da koyarwa akasarsa yana tafiya Dede da zamani ma'ana ansami kyakkyawan tsarin koyarwa hadi da kayan koyo nazamani.

  Dan wasan baitsaya nanba yace yadda sauran yan uwansa yan wasa suke kashe kudadensu wajen sayen many an motoci na alfarma gami da Mayan more rayuwa baiga laifinsuba dalili kusa kudinsu ne. Kuma kowa yana da hangar da yaga yafi dacewa yakashe kudinsa, kuma sun cancanta suyi hakan domin kuwa guminsune. Ma ana halal dinsune. Tokuwa shima yana da hanyar kashe nasa kudaden. Hakannema yaga yadace da yaringa taimakawa yan uwansa marassashi. Ta hanyoyi daban daban..

Thursday 1 July 2021

TAQAI TATCEN TARIHIN AUTA*

TAQAI TATCEN TARIHIN AUTA*

Sunana Mukhtar abdullkarem khalid.(Auta), kuma anhaife ni garin ktasinawa unguwar rimi ungogo kano state, 
Nayi karatun firamare dina a katsinawa special primary school, dagana na gangara zuwa karama sakansire dake gari. Jajira. Bayan haka nayi karatun babbar sakandire a a Army day secondary school dake bukavu Barracks dake kurna.
Bayan haka nayi karatun Diploma afanni. Turanci wato English. A makarantar Aminu Kano callage of education and legal studies. AKILS. Wannan atakaice kena. 

 KARATUN ADDINI,
Abangaren karatun addinima ba abarni abayaba shima anyi bakin iyawa, nafara karatun allo agaban margayi ALHAJI MALAM ISAN GABAS DAKE CIKIN GARIN KATSINAWA.Allah yajiqanshi da rahama ameen. To be continued....

Wednesday 12 June 2019

Zawarci babbar musifa ce Inji tsohuwar jarumar Hausa film Hafsat Shehu.

Zawarci babbar musifa ce Inji tsohuwar jarumar Hausa film Hafsat Shehu.

Zawarci babbar musifa ce Inji tsohuwar jarumar Hausa film Hafsat Shehu.
Tsohuwar jarumar Kannywood, Hafsat Shehu ta yi tsokaci akan halin da mata kan shiga idan aka ce suna zawarci.

Hafsat wacce ta kasance mata ga marigayi jarumin Kannywood Ahmed S Nuhu ta bayyana cewa zawarci bala’i da musifa ce domin a cewarta da zaran an kira mace da Bazawara toh shakka babu darajarta da kimarta na raguwa a idanun mutane.
Jarumar tace ya kai har idan aka ce mace bazawara ce sai ka ga kowa yana kaffa-kaffa da ita.
Ta kuma bayyana cewa zaman zawarci na da daci, kuna da kuma cin rai domin a cewarta akwai abubuwan bacin rai a tattare da shi.
Shafin Mikiya na Facebook ya ruwaito inda jarumar ke cewa: “Hakika zawarci bala’i ne, idan mace tana zawarci ta kan shiga halin Ni yasu, darajarta da kimarta raguwa suke, duk inda kace bazawara ce mace to sai kaga ana kaffa-kaffa da ita.
“Zaman zawarci yana da daci da kuna da kuma cin rai, akwai abubuwa da yawa na bacinn rai wanda bazan iya fada ba.”
Mijin jarumar na farko, Ahmed S Nuhu ya rasu ne yan shekarun baya da suka gabata a hanyarsa ta zuwa wajen diramar Sallah da masana'antar kan shirya. Tun bayan rasuwarsa jarumar bata kuma dawowa harkar fim ba.

Tuesday 11 June 2019

Rigima Ta Barke Tsakanin Teema Makamashi DaTsohuwar Jarumar Kannywood Fati Muhd Akan Wani Wai Shi Dino Malaye.

Rigima Ta Barke Tsakanin Teema Makamashi DaTsohuwar Jarumar Kannywood Fati Muhd Akan Wani Wai Shi Dino Malaye.

Rigima Ta Barke Tsakanin Teema Makamashi DaTsohuwar Jarumar Kannywood Fati Muhd Akan Wani Wai Shi Dino Malaye.

Abinda ya hada da jaruma teema makamashi shine domin tayi masa waka itama fati muhd sai tayi mashi shikenan sai abin ya bata ma teema makamashi rai saboda meyasa tuntuni batayi masa sai da ita tayi sannan ba,a dade ba teema makamashi tayi mata wani martani a shafinta na instagram inda ta daura wani hotonta ita da shi Dino malaye a kasa sai ta saka inda kina tunanin soyayya dashi ne toh kima bari kuma wai idan saboda nayi masa waka ne kema kika yi masa to kin samu matsala saboda idan kika ce duk abinda nayi sai kinyi kina cikin wahala wallahi inji teema makamashi take fadama fati muhd amma haryanzu bata maida mata martani bah.

Friday 7 June 2019

Tuesday 4 June 2019

Saratu Gidado Na Nema Wa Tsohuwar Jaruma Bilkin R.K. Agajin Gaggawa.

Saratu Gidado Na Nema Wa Tsohuwar Jaruma Bilkin R.K. Agajin Gaggawa.

Saratu Gidado Na Nema Wa Tsohuwar Jaruma Bilkin R.K. Agajin Gaggawa.

Post by <> samaila umar lameedo

Ga abin da fitacciyar jaruma Hajiya Saratu Gidado (Daso) ta rubuta:
"Wannan baiwar Allah da mu ka yi hotuna da ita sunan ta BILKIN R.K.
Tsohuwar jarumar films din Hausa ce. Ta yi zamani da su Hindatu Bashir da marigayiya Biba. Ta bada gudunmawa sosai don ci-gaban films.
Ta na fama da ciwon sabara da ciwon kirji da "low blood". Ta rame sosai. Ba ta da mai taimako sai Allah. Ga ta marainiya kuma ba ta da d'a, ga shekaru sun hau mata.
Wanda Allah ya nufa ya na iya taimaka mata da kudin magani ko kayan abinci.
Ga lambar wayar ta nan 08036144627 mai so ya yi magana da ita.
Ko kuma ta bank details di na:
Saratu Gidado
Zenith Bank
1003795458
Ita ta ba ni izini in sanar wa jama'a ko za a dace.
Allah ya bada ikon taimakawa."👏
Sources:Fim magazine
Ki dunga Jan Hankali maigidanki Idan kun zo wajen kwanciya – Obasanjo Ga Aisha Buhari.

Ki dunga Jan Hankali maigidanki Idan kun zo wajen kwanciya – Obasanjo Ga Aisha Buhari.

Ki dunga Jan Hankali maigidanki Idan kun zo wajen kwanciya – Obasanjo Ga Aisha Buhari.

Post By: samaila umar lameedo

Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo yace uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, tayi namijin kokari da ta bayyana gazawar gwamnatin maigidanta
- Obasanjo ya bukaci Aisha da ta dunga tadi da maigidan nata idan sun zo kwanciya don jan hankalinsa akan abubuwan da ke wakana a kasar
- A kwanan nan ne Aisha ta caccaki shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya da kuma tsarinta na magance lamarin ta’addanci a yankin arewacin kasar Tsohon Shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo yace uwargidar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, tayi namijin kokari da ta bayyana wuraren da gwamnatin maigidanta ta gaza.
A kwanan nan ne Aisha ta caccaki shirin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya da kuma tsarinta na magance lamarin ta’addanci a yankin arewacin kasar. Don haka a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, Obasanjo ya bukaci Aisha da ta dunga tadi da maigidan nata idan sun zo kwanciya a matsayin hanyar jan hankalin Shugaban kasar domin sanar dashi rashin jin dadinta akan abubuwan da ke wakana a kasar.
A wani jawabi daga hadiminsa, Kehinde Akinyemi, Obasanjo yayi maganar ne lokacin da ya taka rawar mai masaukin baki na hukumar tantancewa na wata kafar sadarwa, wato Penpushing Media a dakin karatunsa na Abeokuta.
Majiyarmu tat samu wannan daga jaridar legit.ng/hausa a jinjina wa uwardidar Shugaban kasar, cewa matsayarta abune mai kyau ga ci gaban kasar.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Muhammad Yayi Sanarwa.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Muhammad Yayi Sanarwa.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Muhammad Yayi Sanarwa.

Labarin da muke kawo muku kai tsaye daga fadar mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Abubaakar Sa'ad na nuna cewa an ga sabuwar jaririyar watar Shawwal, a yau Litinin 29 ga watan Ramadan wanda yayi daidai da 3 ga watan Yuni, 2019.
Sarkin Musulmi ya sanar da cewa gobe, ranar Talata ce 1 ga watan Shawwal kuma Sallar Idi
Yace: Bisa ga shari'ar Musulmi, muna masu sanar muku da cewa a yau Litinin 3 ga watan Yuni 2019 wanda yayi daidai da 29 ga watan Ramadan 1440, ne karshen watan Ramadana na shekarar 1440AH."
"Mun samu rahotannin tabbacin ganin wata daga shugabannin adinin Musulunci daga gari daban-daban.. Mai martaba Shehun Borno, Sarkin Gwandu, Sarkin Jema'a, Sarkin Damaturu, da wasu sa sassan jihar sokoto
Bisa da haka, gobe Talata 4 ga watan Yuni, 2019 ta zama 1 ga watan Shawwal 1440AH kuma ranar Sallah. Muna rokon Allah ya karba ibadun da mukayi a cikin watar Ramadan."
Source: Legit
Rikici ya barke tsakanin Fati Muhammed da Teema Makamashi akan soyayyar Sanata Dino Melaye.

Rikici ya barke tsakanin Fati Muhammed da Teema Makamashi akan soyayyar Sanata Dino Melaye.

Rikici ya barke tsakanin Fati Muhammed da Teema Makamashi akan soyayyar Sanata Dino Melaye.

An dai ga Teema Makamashi tana habaici a shafinta na Instagram inda
Duka 'yan matan sun yiwa Sanatan waka da fasta ta siyasa sun kai masa, inda ya dauki hoto da kowaccen su
Wani rikici da ya barke tsakanin matan Kannywood guda biyu Teema Makamashi da Fati Mohammed, inda suke rikici akan Sanatan jihar Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye.
Rikicin ya samo asali ne lokacin da Teema Makamashi take gargadin Fati Mohammed akan kwaikwayenta da tayi wurin yiwa Sanatan waka.
Ga abinda Teema Makamashi ta rubuta a shafinta na Instagram:
"Keda samun soyayyarsa sai dai ki gani daga nesa"
Tauraruwar Teema Makamashi wacce ita ce ta fara yiwa Sanata Dino Melaye waka, tayi wannan habaicin ne ga Fati Mohammed wacce ta kwafeta.
Teema tayi rubutun ne a shafinta na Instagram inda ta cigaba da cewa, "Ga wani sabon salon shima idan zaki yi, banda waka, tunda kome nayi sai kinyi, kina tare da bakar wahala indai ni zaki dinga kwaikwaya.

Sunday 2 June 2019

Friday 31 May 2019

Tuesday 28 May 2019

Sunday 26 May 2019

Thursday 23 May 2019

Friday 17 May 2019

Adam A Zango Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Nake Auri saki .

Adam A Zango Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Nake Auri saki .

Adam A Zango Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Nake Auri saki .

Fitaccen jarumin nan na dandalin shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A Zango wanda aka fi sani da Prince Zango ya bayyana dalilin da ya sa yake yawan auran mata kuma daga bisani ya rabu da su. Jarumin ya bayyana cewa ba wai baya iya zama da mace bane, sai dai
ba zan iya fada muku abin da ya hada shi da matata ta farko, da matata ta biyu da kuma matata ta uku ba.
Allah yana hada mata, mace da namiji. Allah ya halicci mata domin su kasance ni’ima a garemu maza. Don mu Allah ya halicce su.
Adam ya kuma bayyana cewa Allah ya rigada ya tsara ma mutum kaddararsa da abunda zai faru da shi tun kan a haifasa har izuwa ranar da zai amsa kiran mahallicinsa.
Dan wasan ya bayyana hakan ne a hira da yayi da shafin BBC Hausa inda yake cewa:
Allah Ubangiji ya rubuta wa mutum abin da zai faru da shi tun daga farkon haihuwarsa har zuwa ranar mutuwarsa.
Kuma wannan kaddarar da Allah yayi mun itace tawa, saboda ni , Allah yana gani, Allah ya ba ni komai da na roke shi, amma ban da mace wanda nake zaman aure da su.
“Sannan kuma ina so na gayawa mutane wani abu cewa, duk mutin da ya kasance zai yi aure ya rabu da mace, ya kara yi kuma ya kara rabuwa da ita, toh ya kamata su gane cewa wannan mutumin ba mazinaci ba ne. Saboda ni Adamu Zango Allah ya ba ni, duk duniya a cikin masana’antar Kannywood, babu wanda mata ke so iri na. Toh me zan yi da aure.
Gwamnatin Jihar Kano Zata Yiwa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi <> Canji Masarauta A Gobe Asabar.

Gwamnatin Jihar Kano Zata Yiwa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi <> Canji Masarauta A Gobe Asabar.

Gwamnatin Jihar Kano Zata Yiwa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi <> Canji Masarauta A Gobe Asabar.


Rahotonnin da suke shigo mana na nuni da cewar, a gobe Asabar ne gwamnan Kano Ganduje zai yiwa Mai Martaba Sankin Kano Muhammadu Sanusi II canjin masarauta.
Majiyar mu, wadda wani makusancin gwamnatin da ya nemi a sakaye sunansa, ya shaidawa wakilin mu cewar, gwamnatin ta gama shirinta tsaf gobe Asabar domin mayar da Sarki Sanusi II Bichi tare da maye gurbin masarautar ta Kano da sabon Sarkin Bichi Aminu Ado Bayero.
Majiyarmu hausaloaded ta ruwaito wannan labari daga madubi h Saidai da muke jin ra'ayin jama'a, mafiya yawa sun bayyana rashin goyan bayansu akan wannan abinda yake faruwa tsakanin masarautar Kano da gwamnatin jihar Kano.
Rigima Ta barke tsakanin mawaki Naziru Ahmad da jarumar Fim Hadiza Aliyu Gabon.

Rigima Ta barke tsakanin mawaki Naziru Ahmad da jarumar Fim Hadiza Aliyu Gabon.

Rigima Ta barke tsakanin mawaki Naziru Ahmad da jarumar Fim Hadiza Aliyu Gabon.

Rigima Ta Barke Tsakanin Naziru Da Gabon.

Naziru Ahmad sarkin wakar sarkin Kano yayi wani shagube kan masu kyauta suna yadawa a kafafen sada zumunta na zamani inda yake cewa “Yin hakan bai kamata ba saboda cin fuska ne ga wanda kake bawa sadakar kuma kana yada shi.
Ba tare da jimawa ba ita ma jaruma Hadiza Aliyu Gabon ta maida martani inda take cewa Ya kamata ayi kyauta a bayyana domin wasu suyi koyi da taimakawa marasa karfi.


Kotu ta bada dama kwamishinan yan sanda da ya kamo hadiza Gabon.

Kotu ta bada dama kwamishinan yan sanda da ya kamo hadiza Gabon.

Kotu ta bada dama kwamishinan yan sanda da ya kamo hadiza Gabon.

A yaune Alhamis mai shari'a muntari dandago na kotun magistrate court 15 dake zamanta nomansland ya bawa komishinan yan sanda na jihar kano umarni ya kamo shahararriyar jarumar wasan Hausa hadiza Gabon sabida taki amsa kiran kotun.
Mustapha na buriska shine ya shigar da karar jarumar yana zarginta da cewa tanayi masa barazana da rayuwa ya yanke shawarar maka ta kai tsaye zuwa kotu saboda saboda yana tsoron idan ya kaiwa hukumar yan sanda bazata tuhme ta ba kasancewar yadda jarumar takeda mu'amala da wasu daga cikin jami'an yan sanda da kuma manyan yan siyasa dama masu kudi a fadin kasar nan.
Mai shari'ar ya bada umarnin hakan saboda bijirewa gayyatar da kotu ta 1 tayi mata kuma ya kara da cewa idan kwaminshinan yan sanda ya kamata ya tabbatar an binciketa akan lainfin da mai karar ya shigar kafin a damkata ga hannun kotun suma suyi nasu hukuncin.

Thursday 16 May 2019

Wednesday 15 May 2019